Manchester za ta saki Pogba, Messi na tattaunawa da Barca

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na gab da cimma yarjejeniyar da za ta ba ta damar dauko Gareth Bale daga Real Madrid a watan Janairu, yayin da ita kuma Man Utd din za ta bai wa Madrid Paul Pogba. (Sun on Sunday)
PSG na nuna sha'awarta na sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Liverpool Adam Lallana. (Sunday Mirror)
Arsenal na shirin taya dan wasan baya na kasar Turkiyya Merih Demiral, amma idan ba ta yi hankali ba za a iya sayar da shi ga Juventus idan Juve din ta ajiye kudi mai tsoka. (Tuttosport - in Italian)
Barcelona na tattaunawa kan sanya hannu a sabon kwataragi tsakaninta da dan wasa Lionel Messi. (Mondo Deportivo - in Spanish)
Zlatan Ibrahimovic na neman a rinka biyan sa kudi Fan 900,000 a kowane wata, ga duk kungiyar da ke son ta saye shi domin dawowa buga wasa a Italiya. Kungiyoyin Inter Milan, da Bologna, da kuma Napoli ne dai ke neman sayo tsohon dan wasan na LA Galaxy da Man Utd. (Mail on Sunday)
Manchester City na tunanin sayo Kingsley Coman daga Bayern Munich matukar Leroy Sane ya kuma Munich din a lokacin musayar 'yan wasa. (Sky Sport)







