Hazard da Hazard sun ci wa Belgium wasa

Thorgan Hazard da Eden Hazard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Thorgan Hazard wanda ke wasa a Dortmund yana murnar cin kwallo tare da dan uwansa Eden na Real Madrid

Eden Hazard ya ci kwallo biyu a wasan da kasarsa Belgium ta casa kasar Russia ranar Asabar yayin da Belgium din ke ci gaba da jan zarenta a wasannin cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020.

Belgium wadda tuni ta samu gurbin shiga gasar, ta ci kwallo uku tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, guda biyu ta kafar Eden Hazard da kuma daya daga dan uwansa Thorgan Hazard.

Daga baya Romelu Lukaku na Inter Milan ya kara ta hudu kafin daga bisani Georgi Dzhikiya ya farke wa Russia kwallo daya.

Dedryck Boyata da Michy Batshuayi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dedryck Boyata (mai lamba 4) ya shiga filin wasan sanye da jesin Michy Batshuayi kafin daga bisani ya sauya sannan kuma Batshuayi ya shigo wasan

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma dan wasan bayan Belgium Dedryck Boyata ya fito sanye da jesin Michy Batshuayi (lamba 23), kafin daga bisani ya saka tasa bayan minti 13.

Batshuayi ya shigo wasan daga baya sanye da jesinsa mai lamba 23.

A ranar Talata ne Belgium za ta kammala wasannin a rukuni na 1 tsakaninta kasar Cyprus.

Russia kuwa wadda ita ma tuni ta samu gurbin, za ta kammala nata wasannin ne da San Marino ranar Talata da misalin karfe 7:45.