Ce-ce-ku-cen VAR: 'Akwai bukatar a sauya wasu dokoki'

VAR

Asalin hoton, Getty Images

Wani jigo a Gasar Premier ta Ingila ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar a sauya wasu dokoki domin rage samun ce-ce-ku-ce kan na'ura mai taimaka wa alkalin wasa VAR.

A wannan zangon wasan ne aka kawo VAR, amma mutane sun yi Allah-wadai da wasu hukunce-hukuncen VAR da daukar lokaci da ake yi kafin a yanke hukunci.

A ranar Alhamis ne aka sanar da manyan kungiyoyin kwallo cewa ba za a samu wani sauyi ba a wannan zangon.

"Za a iya magance wannan ne kawai ta hanyar fahimtar dokoki sosai" kamar yadda ya ce.

Gasar ta fitar da wani tsari domin yanke hukunci kan cin kwallaye da fenariti da ba da jan kati da kuma satar gida.

An dade ana tattaunawa a kan lamarin satar gida har da na dan wasan gaban Liverpool Roberto Firmino, a wasansu da Aston Villa a ranar 2 ga watan Nuwamba wanda aka yanke cewa satar gida ne, saboda kafadarsa ta wuce gwiwar dan bayan Tyrone Ming.

Dokokin FA sun ce "kowannen sashen kai ko jiki ko kuma kafa za a iya cewa satar gida ne.

Wani alkalin wasa yana duba na'urar VAR

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani alkalin wasa yana duba na'urar VAR

Daga cikin tsokacin da ake yi wa VAR ya hada da rashin shigo da 'yan wasa da masu timaka wa alkalin wasa da ke a gefe.

A ranar 10 ga watan Nuwamba aka hana wa Manchester City fenariti inda suke zargin cewa kwallo ta taba hannun dan wasan baya Trent Alexander Arnorld, inda Liverpool ta ci su uku da daya a wasan da suka buga a gida a Anfield.