Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hazard da Hazard sun ci wa Belgium wasa
Eden Hazard ya ci kwallo biyu a wasan da kasarsa Belgium ta casa kasar Russia ranar Asabar yayin da Belgium din ke ci gaba da jan zarenta a wasannin cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020.
Belgium wadda tuni ta samu gurbin shiga gasar, ta ci kwallo uku tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, guda biyu ta kafar Eden Hazard da kuma daya daga dan uwansa Thorgan Hazard.
Daga baya Romelu Lukaku na Inter Milan ya kara ta hudu kafin daga bisani Georgi Dzhikiya ya farke wa Russia kwallo daya.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma dan wasan bayan Belgium Dedryck Boyata ya fito sanye da jesin Michy Batshuayi (lamba 23), kafin daga bisani ya saka tasa bayan minti 13.
Batshuayi ya shigo wasan daga baya sanye da jesinsa mai lamba 23.
A ranar Talata ne Belgium za ta kammala wasannin a rukuni na 1 tsakaninta kasar Cyprus.
Russia kuwa wadda ita ma tuni ta samu gurbin, za ta kammala nata wasannin ne da San Marino ranar Talata da misalin karfe 7:45.