Abokan wasan Sane suna zuga shi ya koma Bayern Munich

Abokan wasan Leroy Sane na kungiyar Manchester City na ci gaba da zuga dan wasan na kasar Jamus mai shekara 23, cewa ya bar kungiyarsa ya koma Bayern Munich a badi. (Telegraph)

Manchester United za ta zuba kudi don sayo dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho mai shekara 19 a watan Janairu, yayin da rashin jituwa ke kamari tsakanin sa da Borussia Dortmund. (Guardian)

Dan wasan tsakiya na Arsenal Dani Ceballos, mai shekara 23, zai ki komawa Real Madrid idan dai har Zinedine Zidane zai ci gaba da zama kocin kungiyar. (Sun via AS)

A shirye Manchester United take ta kawo dan wasan gaban kungiyar Red Bull Salzburg, Erling Braut Haaland mai shekara 19, bayan da farashin dan wasan ya yi tashin gwauron zabi a kashi na farko na kakar wasan bana. (ESPN)

Kungiyar Red Bull Salzburg za ta sanya farashin euro miliyan 100 kan Haaland, wanda da ne ga tsohon dan wasan tsakiyar kungiyoyin Leeds da Nottingham Forest da Manchester City, wato Alf-Inge. (AS)

A shirye Manchester United take ta bayar da aron Haaland ga Red Bull Salzburg idan dai har za ta iya cimma yarjejeniya a kan dan waan gaban a watan Janairu. (Mirror)

Amma an yi amannar cewa watakila Haaland ya fi son koma wa Real Madrid ko Barcelona. (Mirror)

Manchester City na da sha'awar cimma yarjejniya kan dan wasan Leicester da Ingila Ben Chilwell mai shekara 22, bayan da Benjamin Mendy mai shekara 25 ya kasa tabuka abin arziki. (90min)

Mahaifin dan wasan gaban Everton dan Italiya Moise Kean mai shekara 19, yana son dansa ya barkungiyarsa ya dawo Italiya. (Sun)

Real Madrid ta matsu ta sayo dan wasan Chelsea mai shekara 19 Callum Hudson-Odoi. (Mirror, via El Desmarque)

Haka kuma Real Madrid din na sa ido kan Haaland da Kean da kuma dan wasan Villarreal dan Najeriya mai shekara 20, Samu Chikwueze. (Star)

Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 34, zai tattauna da Juventus bayan da ya nuna fushinsa kan sauya shi da aka yi a wasan makon jiya. (Mirror via Gazzetta dello Sport)