Haryana: Kananan yara amare da ke cike da burin rayuwa a Indiya

Asalin hoton, Ruhani Kaur
Yar jarida mai daukar hoto Ruhani Kaur ta bi diddigin labarin kananan yara amare daga jihar Haryana da ke arewacin kasar Indiya da ke cike da burin karatu da kuma aiki duk kuwa da wani abu ne mai kamar da wuya.
Priyanka, da Meenakshi da Shiwani sun girma a kauyen Damdama, wanda ke da yawan al'ummar Gujjar, shahararrun al'ummomin manoma.
Kauyensu na da nisan kasa da sa'a daya daga garin Gurgaon, da ke wajen Delhi babban birnin kasar.
'Yan matan masu kimanin shekaru 16 sun kasance kawayen juna tun suna kanana. Suna sun taba zama kananan amare - daya an yi mata aure lokacin tana da shekara 10 kacal.
Karya doka ne a aurar da 'yan matan da shekarunsu bai kai 18 ba a Indiya. Amma har yanzu ana ci gaba da gudanar da wannan al'ada saboda talauci da kuma fifita maza.
Indiya kasa ce da aka fi samun yawaitar kananan yara amare a duniya, da aka kiyasta a kan daya bisa ukun na daukacin duniya, kamar yadda Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya bayyana.
Kugiyar ta kididdige cewa 'yanmata 'yan kasa da shekara 18 akalla miliyan daya da rabi ne ake yi wa aure a kowace shekara.
A shekarar da ta gabata, gwamnati ta gabatar da kudiri a majalisar dokoki ta kara yawan shekarun aure zuwa 21, amma har yanzu bai zama doka ba.
Kawayen biyu suna da matukar son yin rayuwar 'yanci, amma kuma sun san cewa akwai babban kalubale a gabansu.


'Ka da ku ɗaure ni da aure'
Shekarun Priyanka 10 lokacin da iyayenta suka yi mata aure. Bayan shekaru bakwai, tana aji na 11, kuma tana cigaba da zama a gidan iyayenta.
Amma an fada mata cewa za ta koma zama tare da mijinta - wanda ke karatun jarrabawar shiga aikin dan-sanda - da zarar ya samu aiki.
Tana fargaba, kuma ta rubuta damuwarta a cikin dan littafinta.
"Ka da ku daure ni da aure,'' na yi kankanta… Ba na son zuwa wurin surukata in bar 'yartsanata a gida,'' ta rubuta.
Priyanka ta ce ba ta da kokari wajen karatu sosai, amma tana taimaka wa a wurin gyaran jiki na yayanta - tana cike da burin hakan zai taimaka mata kara tsawaita zamanta a gida.
Yaruwarta - wacce ta auri danuwan mijin Priyanka - ita ma ta koyi yadda ake gyaran jiki amma ba ta iya ci gaba ba saboda an yi mata aure. Priyanka tana son sauyin rayuwa ta daban.

'Bai kamata mu yi aure ba har sai burinmu ya tabbata'
A shekarar da ta gabata, lokacin da Meenakshi ta shiga aji na 11, ta yi ta daya a makarantarsu da ta shiga fannin kimiyya. Farin cikinta ba ya misaltuwa, ta bayyana.

Asalin hoton, Ruhani Kaur
A wannan mataki, annobar korona ta sauya rayuwar mutane. Miliyoyi sun rasa aikinsu lokacin kullen tsawon lokaci, a yayin da dama suka koma garuruwa da kauyukansu.
Har ila yau lokaci ne iyayen 'yan mata da dama, da suka damu game da makomarsu ke tsara yi musu auren hadi.
Abokan karatun Meenakshi da dama an yi musu aure lokacin kullen, amma tana fatan dan dakatawa. '' Ban san wani abu game da shekarun da suka dace (a yi aure ba) amma har sai burinmu ya tabbata, bai kamata mu yi aure ba!" ta bayyana.
Amma a ranar 5 ga watan Fabarairu, ta zama daya daga cikin wadannan alkaluma.
Har yanzu ana iya ganin lallen da bai gama gogewa ba a hannuwan Meenakshi a lokacin da ta yi kokarin dauko wayar salularta, wacce karan sakonni ke shigowa ciki daga mijinta mai shekara 16.
Jajayen warwarayenta na kara a lokacin da ta ke kokarin rubuta masa amsa.
Mijinta shi ma karatu yake yi, don haka iyayen Meenakshi sun shaida mata cewa za ta iya ci gaba da zama a makaranta yanzu. Tana mai fatan iyayenta da surukanta za su amince ta ci gaba da karatunta har iya yadda take so.

Burin aikin banki
Akwai alamar farin ciki a fuskar Shiwani lokacin da take magana game da karatu - tana son zuwa makaranta kana tana da burin zama ma'aikaciyar banki.

Asalin hoton, Ruhani Kaur
Amma lokacin da mahaifiyarta ta fito da littafin hotunan aurenta daga cikin kabad, Shiwani ta koma cikin hayyacinta kan gaskiyar lamari. Ta san cewa ba lallai ba ne ta zamana tana iko kan makomarta bayan ta kammala aji 12.
An yi wa Shiwani da yayarta Ashu aure a rana daya - kawunsu ne ya hada auren tare da sauran yayansa mata, bayan da mahaifinsu ya kwanta rashin lafiya.
"Babu wani abu da ya sauya. An aurar da ni ina da shekara 15, haka ma diyata,'' in ji mahaifiyar Shiwani.
Mahaifinsu ya yi alkawarin kyale su su kammala aji 12, don haka duka 'yanuwan junan na cike da buri.

Asalin hoton, Ruhani Kaur
Ashu ta tafi gidan mijinta kafin sakamakon jarrabawa ya fita. Tana son ta karo karatu, watakila ma ta yi karatun lauya, kana tana fatan surukanta za su amince.
Amma a cikin 'yan watanni, ta samu juna biyu. Ta haihu a farkon wannan shekarar.

Asalin hoton, Ruhani Kaur
A yayin da rayuwa ke ci gaba a kauyen, a lokacin bazara, Priyanka, da Shiwani da kuma Meenakshi sun hadu da kawarsu Monu, wacce ta tsira daga matsin lambar yi mata aure.
Sun yi wani ihu cikin mamaki a yayin da suke yawa a cikin wani lilo.
A yayin da suka fara juyawa da lilon da sauri-sauri, 'yanmatan sun manta da damuwarsu na dan wannan lokacin jin dadi.
Wannan aikin ya samu goyon bayan Asusun Ƙungiyar Ilimin Ƙasa na Gaggawa ga Yan Jarida
Dukkan hotonan na da haƙƙin mallaka.














