An kama mutumin da ake zargi da yi wa tsohuwa mai shekara 87 fyaɗe a Indiya

The woman, who is bed-ridden, was alone when the man broke into her house and attacked her.

Asalin hoton, Getty Images

An kama wani mutum mai shakara 30 da laifin yi wa wata mata mai shekara 87 fyaɗe a Delhi, babbar birnin Indiya.

'Yan sanda sun ce mutumin na aikin shara ne wanda yake zama kusa da gidan matar a unguwar Tilak Nagar.

'Yan sandan sun ƙara da cewa matar, wadda tsufa da jinya suka kwantar, ita kaɗai ce a gida a ranar Lahadi da yamma lokacin da aka kai mata harin tare da yi mata fashi.

Ƴan uwan tsohuwar sun ce laifin 'yan sanda ne, da tun farko suka shigar da ƙorafin fashin ban da na fyaɗen - sai dai 'yan sanda sun ce ba haka ba.

'Yan sanda sun ce iyalan matar sun kawo ƙarar fashi ne kawai a ranar Lahadi- sai daga baya suka kawo na fyaɗe kuma a ranar Litinin.

Ɗaya daga cikin dangin matar ya faɗa wa jaridar Indian Express cewa 'yan sanda sun ce wa matar da ƴarta da ka da su bibiyi ƙorafin fyaɗen saboda zai ba su wahala. "Yan sanda sun shigar da ƙorafin sata kuma ba su gaya mana ba ma," in ji mutumin.

Matar na zama ne a gidan tare da ƴarta, wadda ba ta gida a lokacin da abun ya faru. Da ta dawo ne ta sami mahaifiyarta da raunuka.

Hukumar kula da mata ta ƙasa ta ce a ranar Litinin ɗin da ta gabata ta rubuta wa ƴan sandan Delhi wasiƙar neman a ɗauki matakin hukunta jami'an da ake zargin ba su dauki matakin gaggawa ba.

A shekarar 2020, wani fyaɗen da aka yi wa wata tsohuwa mai shekara 86 a Delhi- ya girgiza mutanen ƙasar.

Fyade da cin zarafi ya fara fitowa fili ne a Indiya tun a shekarar 2012, lokaicin da wasu gungun mutane suka yi wa wata budurwa fyaɗe tare da kashe ta a cikin motar bas a Delhi.

Presentational grey line

'Ba wanda ya tsira'

Geeta Pandey, BBC News

Bayan da aka yi ta ce-ce-ku-ce a faɗin duniya kan irin mummunan fyaɗen da aka yi wa wata mata a motar bas a birnin Delhi a watan Disambar 2012, Indiya ta ɓullo da wasu tsauraran dokoki na fyaɗe da suka hada da hukuncin kisa musamman a manyan laifuka, ta kuma yi alkawarin kafa kotuna cikin gaggawa don yin shari'ar fyade.

Sai dai masu fafutuka sun ce al'amura ba su canza sosai a kasar ba.

"Al'amarin bai canza ba saboda kare mata da 'yan mata ya kamata a sa gaba a jerin abubuwan da gwamnati za ta duba, amma ba a kai ga yin hakan ba," in ji Yogita Bhayana, mai fafutuka tare da mutanen da ke zanga-zanga a kan fyade a Indiya (Pari), wata kungiya mai zaman kanta.

Ms Bhayana ta ce "babu wani sihiri ko wani abu" da zai iya sa matsalar cin zarafin mata ta dauke kamar ƙiftawar ido.

Ta ce akwai bukatar a sauya abubuwa da yawa - ƴan sanda da gyaran shari'a, da ƙara wayar da kan 'yan sanda da lauyoyi, da ingantattun kayan aikin bincike.

"Amma fiye da komai, muna bukatar wayar da kan mata da maza, mu yi aiki don sauya tunani, don hana faruwar irin wadannan laifuka tun da farko."

"Na hadu da wata yarinya 'yar wata daya da mata 'yan shekara 60 da aka yi wa fyade," in ji ta, ta kara da cewa babu wanda ya tsira.

Presentational grey line
Presentational grey line