Yadda tsawa ke kashe dubban mutane a Indiya

Asalin hoton, Getty Images
Cikin mintoci kadan wani haske ruwan dorawa ya biyo ta cikin bishiyar tare da tsananin karar tsawa.
Galibi dai cikin dakika daya ne tsawar kan faru. Kuma akasari hasken tsawar na da karfin wutar lantarki 300 da karfin 30,000 amps - da ke kisa nan take. Takan haddasa duk iskar da ke kewaye da ita dumama yanayin zafin da ya linka sau biyar fiye da na saman rana.
Mutanen hudu sun fadi kasa. Daya daga cikinsu yam utu, yayin da sauran suka tsira da kuna.
"Ba zan iya tuna abinda ya faru da ni ko yadda ya faru ba. A cikin dakikoki komai ya wargaje,'' wanda ya rayun ya shaida wa wata jarida.
Abokan aikinsa wasu daga cikin Indiyawa fiye da 2,500 ne da ke rasa rayukansu a ko wace shekara.
Faduwar tsawa ta hallaka mutane fiye da 100,000 a kasar tsakanin shekarar 1967 da 2019, kamar yadda alkaluman binciken hukuma suka nuna.
A cikin watan Maris din shekarar da ta gabata, wasu masu aikin lambu hudu da ke a wani rukunini gidaje a gundumar Gurgaon, yankin da ke kusa da Delhi babban birnin kasar Indiya, suka fake a karkashin wata bishiya sakamakon saukar ruwan sama.
Wannan fiye da daya bisa ukun mace-macen da ake samu ta wannan hanyar ne a wannan lokaci.
Wadanda suka tsira kan cigaba da rayuwa da alamun cututtuka irin su kasala, da jiri, da cutar mantuwa.
Shekaru uku da suka gabata ne Ofishin lura da yanayi na kasar Indiya ya soma gudanar da hasashe kan tsawar.
Yanzu akwai manahajojin wayar salula da ke bin diddigin hasken tsawar. Ana kuma ankarar da mutane ta cikin rediyo, da talabijin, da kuma masu aiki sa kai.
Wani gangamin da aka shafe shekaru uku ana yi na wayar da kan jama'a game da tsawar na kasar Indiya da ake kira Lightning India Resilient, na aiki tukuru wajen fadakarwa a kauyukan da suka fi fuskantar barazanar faduwar tsawa tare da yawan rage mace-mace.

Asalin hoton, Getty Images
Amma kuma, an kara samun yawaitar faduwar tsawar matuka. Kasar Indiya ta shaida faduwar tsawar fiye da imliyan 18 a tsakanin watan Aprilun shekarar 2020 da Maris din shekarar 2021, kamar yadda wanni bincike da kungiya mai zaman kan ta kan yanayi ta Climate Resilient Observing Systems Promotion Council ta bayyana.
Wannan karuwar kashi 34 bisa dari ne idan aka kwatanta da lokaci irin sa a shekarar da ta gabace ta.
Alkaluman bayanan tauraron dan adama daga cibiyar binciken yanayi da kasar Indiya suma sun nuna cewa faduwar tsawar da ''karu matuka'' tsakanin shekarar 1995 da 2014.
Duk da cewa rabin gwamman jihohi sun shaida yawan abkuwar tsawar, jihohi uku - Odisha, da Jharkhand da kumaWest Bengal - sun shaida kashi 70 bisa dari na mace-mace. Mazan da ke aiki a gonaki sun fi fuskantar hadari.
"Akwai yawan tsawa a yankinmu. Har yanzu ina iya tuna wani karamin yaro mai shekara bakwai da ya rasa ransa lokacin da ya fita don debo wa shanunsu ruwa.
Yanzu muna kokarin zama a cikin gida,'' in ji Sandhyarani Giri, wata malamar makaranta a West Bengal.
Mis Giri na zaune ne a kauyen masunta mai cike da jama'a yankin Fraserganj da ke kan iyaka da Bay of Bengal, mai nisan kilomita 120km (mil 74) daga kudancin babban birnin Kolkata.
Wuri ne da ake yawan samun faduwar tsawa - mutane kusan 60 ne ke mutuwa a ko wace shekara sakamakon tsawar a gundumar South 24-Parganas, inda kauyenta yake.
Kauykan bakin teku na da filaye masu fadi da kuma ruwa: gonaki, da kududdufai da gidajen da masu rufin kwano da ciyayi.
Zama a kusa da teku kan kasance da hadarin gaske: karuwar abkuwar mahaukaciyar guguwa da ambaliyar ruwa tamkar ruwan dare ne.
Akasari faduwar tsawa ta fi faruwa a kan sararin kasa, amma ta kan shafi ruwan tekuna ma.
Tsawa kan faru ne sakamakon wutar lantarkin da ke fita wacce akasari rashin daidaito a tsakanin guguwar hadari ke haddasawa.
Don haka mazauna kauyuka sun taimaka wajen fadakar da jama'a kan rage mace-macen sakamakon tsawa ta hanyar kakkafa turakun kawar da faduwar tsawar kan doron kasa da suke hadawa a gidajensa.

Asalin hoton, Ronny Sen

Asalin hoton, Ronny Sen

Asalin hoton, Ronny Sen

Asalin hoton, Ronny sen
Mazauna kauyuka kan yi amfani da karafunan rim tayoyin keke da aka gama amfani da su, da itacen bamboo da wayoyin karfe wajen hada wannan turakun tsawar.
Ana kafa karfen rim din tayar a kan turken itacen bamboo - a wasu lokutan tsawonsu kan kai kafa 30 - da ake daurawa a jikin gine-gine, akasari a makarantu da cibiyoyin taruwar jama'a.
Turakun kan tabbatar da ganin wutar lantarkin da ke fita daga tsawar ta sauka cikin kasa ba tare da hafar da wata illa ba.
Mutane da dama da faduwar tsawar ta shafa a Indiya na zaune a kauyuka ne kuma na mutuwa ne sakamakon fakewa a karkashin bishiyoyi, kamar yadda binciken da kungiyar wayar da kai kan tsawa Lightning Resilient India Campaign ta bayyana.
Kabilu wadanda ke ayyukan noma da kamun kifi da kuma fadi tashin neman abinci sun fi fuskantar hadari.
Fafutikar da kungiyar ke yi ta haifar da raguwar mace-macen sakamakon tsawar da kashi 60 bisa dari a wasu jihohin.
"Amma akwai rashin wayar da kan al'umma sosai kan abubuwan da suka shafi kariya daga bangaren gwamnatoci wajen kai wa ga ainihin mutanen da suka fi fuskantar hadari a yankunan da aka fi samun tsawar kamar gonaki, da dazuka, da bakin teku, da kududdufai, da kuma kogwanni,'' in ji Kanal Sanjay Srivastava, jagora a kungiyar.
Masana kimiyya sun ce barazanar sauyin yanayi na kara ta'azzara yawan abkuwar tsawar.
Karuwar yanayin zafin a doron kasa da kan teku da isakar saman a kara zafafa makamashin da ke haddasa tsawar daga inda hadari mai dauke da tsawar a ciki.
Wani bincike da masana kimiyya suka gudanar a Jami'ar California, Berkeley ya yi nuni da cewa faduwar tsawa a Amurka za ta iya karuwa da kashi 12 bisa dari kan ko wane karuwar ma'aunin zafi.
A kasar Indiya, karuwar birane da karancin tarin bishiyoyi wuri guda kan haifar da karuwar yanayin zafi

Asalin hoton, Getty Images
"Zafi a kan doron kasa, da danshi a saman ruwa, da kuma abubuwan feshi saboda gurbacewar yanayi kan haifar da yanayi mai sauki na ta'azzara hadarin da ke haifar da yawan tsawa.
A yayin da Indiya ke kara dumama da kuma gurbata yanayinta, hadari mai tsawa zai karu,'' in ji SD Pawar, daraktan Cibiyar Kula da Yanayi da kuma Sauye-sauyen tsawa a kasar.
Ya kuma ce, karfin faduwar tsawa na karuwa: a baya bayan nan, masana kimiyya sun tabbatar da kusan mil 500 na tatsatsin wutar tsawar da ya rashi zuwa sararin samaniya a fadin jihohi uku na Amurka , tare da kafa sabon tarihi na hasken wuta mafi tsawo.
Kasar Indiya na da burin rage yawan mace-macen da ake samu ta hanyar tsawa zuwa kasa da 1,200 a ko wace shekara nan na shekarar ta 2022.
Masu aikin sa kai na da fafutikar wayar da kan jama'a tare da fada wa mazauna yankunan karkara da su rika zama a cikin gidajensu da kuma kauce wa zuwa ciki budaddun wurare don kiwon dabbobi lokacin saukar ruwan sama ko guguwa.
Suna fada musu kada sun tattaru a karkashin bishiyoyi, kana sun kauce wa wuraren wutar lantarki da shingayen karafuna.
Amma kuma a ko wace shekara, a sararin samaniya, akan shaida tarin haksen wutar tsawar,. '' Abin ban tsoro ne,'' in ji Mis Giri.
Me ya kamata a yi a duk lokacin faduwar tsawa?
- Nemi mafaka a cikjn babban gini ko mota
- Fita daga budaden wuri mai fadi da kuma saman manyan duwatsu
- Idan ka rasa wurin fakewa, ka dunkule kan ka wuri guda ta hanyar hade kafafuwanka wuru daya, da hannayenka a kan guiwa ka cusa kan ka ciki
- Kana ka fake a karkashin dogayen bishiyoyi dake kebe wuri guda
- Idan a kan ruwa ake, ka yi sauri ka nufi inda da za ka sauka a bakin ruwan.
Bayanai daga: Royal Society for the Prevention of Accidents











