Aneera Kabeer: Matar da ta koma namiji ta so kashe kanta saboda ana ƙyamarta

Asalin hoton, Courtesy Aneera Kabeer
- Marubuci, Daga Sharanya Hrishikesh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
A watan Nuwambar bara, Aneera Kabeer ta halarci jarrabawar neman aiki ta 14 watanni biyu da suka gabata sanye da hula, da kuma takunkumi da ya rufe mata fuska sanye da kayan maza.
Matar mai shekara 35, wadda ta mayar da kanta namiji, ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne sakamakon matsuwar da ta yi biyo bayan irin munanan kalaman da aka sha yi mata a jarrabawar neman aikin baya da ta halarta.
Ta samu aiki na wucin gadi a wata makarantar gwamnati da ke a Jihar Kerala da ke kudancin India - sai dai ta yi zargin cewa an yi mata sallamar rashin adalci daga makarantar bayan watanni biyu.
Shugaban makarantar ya ƙi yarda ya yi magana kan wannan batu. P Krishnan, wanda jami'in gunduma ne, ya bayyana cewa shugaban makarantar ya shaida masa cewa ba a sallami Ms Kabeer ba kuma "ba ta fahimci yadda lamarin yake ba".
Bayan ta rasa yadda za ta yi, sai Ms Kabeer ta je wajen hukumar shari'a ta jihar a watan Janairu -ta bayyana cewa tana buƙatar lauya domin shigar da ƙara kan yunƙurin kashe kai a madadinta.
"Abin da kawai nake so shi ne na yi aiki domin na samu abinci. Sai dai hakan ya ƙi yiwuwa," in ji Ms Kabeer.
Ta karanta littafai da suke nuna yadda mutum zai kashe kansa - sai dai Indiya ta bayar da dama ne kawai a kashe kai ba kai-tsaye ba.
"Na san cewa ba zan bari a amince mani a nan ba. Amma ina so a tura saƙo," in ji ta.
Sai dai tana so ta ja hankalin ƙasar - kuma ta ja hankali na ƙarshe. Gwamnatin cikin sauri ta mayar da martani inda a yanzu ta samu wani aikin.
Zanga-zanga...da alƙawura
Ms Kabeer ta fito fili ta bayyana cewa ba ta da niyyar kashe kanta, kuma abin da ta yi ba ta yi shi ba ne don ya zama ishara ga wasu.
Sai dai irin wannan wasan kwaikwayon da ta yi ba a cika samunsa a Indiya ba.
A shekarun da suka gabata, ƴan ƙasar Indiya na ta neman a samu sauyi da yi musu adalci, inda suka yi yajin aikin cin abinci tare da fitowa zanga-zanga ɗauke da lasifika.

Asalin hoton, Getty Images
Masana halayyar ɗan adam sun bayar da shawarar amfani da irin abubuwan kirkin da Mahatma Gandhi ya bari na bore ga gwamnati ta hanyar ƙin tashin hankali wanda ya haɗa da azumi mai tsawo.
Anagha Ingole, wadda take koyar da kimiyyar siyasa a Jami'ar Hyderabad, ta bayyana cewa irin abin da Ms Kabeer ta yi abu ne da ya kamata ya tuna wa gwamnati cewa ta gaza cika alƙawuranta.
"A wannan lamari, ƙasa ta gaza wajen cika alƙawarinta domin tabbatar da ƴan ƙasar sun samu aiki," in ji Ms Ingole wadda ta yi aiki sosai kan lamuran da suka shafi nuna wariya ko bambanci.
An yi ƙiyasin cewa Indiya tana da kusan mutum miliyan biyu waɗanda suka sauya jinsinsy, duk da cewa masu fafutika sun ce adadin ya wuce haka. A 2014, Kotun Ƙolin Indiya ta yanke hukuncin cewa waɗanda suka sauya jinsinsu suna da ƴanci iri ɗaya da sauran jinsi.
Sai dai duk da haka suna shan wahala wajen neman ilimi da lafiya a asibiti. Haka kuma da dama daga cikinsu ana tilasta musu rayuwa ta hanyar bara ko kuma karuwanci.
Ms Kabeer ta bayyana cewa al'umma na buƙatar wakilci na siyasa da kuma gurabe na aiki.
"Ban taɓa neman ɗaukar irin wannan mugun mataki ba, amma wane zaɓi nake da shi?" in ji ta.
Tana ƙoƙarin gwagwarmya da kanta
Girma a gundumar Palakkad da ke tsakiyar Kerala, Ms Kabeer ta bayyana cewa ta yi ta yin gwagwarmaya tsawon shekaru domin ta gano jinsinta na haihuwa.
Ba ta son ta yi magana a kan iyalanta waɗanda ta ce suna ci gaba da jimamin mutuwar ɗan uwanta.
Ms Kabeer ta kasance mai shekaru ƙasa da 20 a lokacin da ta yi iƙiƙarin neman sauran jama'ar da suka sauya jinsin su a Palakkad. Sai dai ta bar yin hakan bayan a yunƙurin nata an kama ta a ƙarshe.
Ta gudu daga gida zuwa birnin Bangalore bayan ganin hotunan waɗanda suka sauya jinsinsu a jarida. Ta gano wata ƙungiyar waɗanda suka sauya jinsinsu waɗanda suka karɓe ta.
Sai dai rayuwa ta kasance mata da wahala - da dama daga cikinsu sun rinƙa bara domin su tara kuɗi tsawon shekaru domin yi musu tiyatar sauya jinsi.

Asalin hoton, Getty Images
Ms Kabeer ta koma gida cikin baƙin ciki.
"Na yi ƙoƙari matuƙa domin na yi rayuwa yadda iyalina suke so na yi," kamar yadda ta tuna da bayyanawa.
Waɗannan sun haɗa da shan sigari da shiga wajen motsa jiki da kuma karatu kan ci gaban kai - waɗanda duka mutanen da ke kusa da ita ke kallo a matsayin za su sa ta zama "namiji sosai".
Ta yi karatu sosai - tana da burin koyarwa tun tana ƙarama kuma ta rinƙa koyar da ƙananan yara a makwafta.
Hakan ya sa ta ci gaba da rayuwa duk da ta bar gida domin yin rayuwar da take so.
A halin yanzu Ms Kabeer na da digiri na masters guda uku, inda ta yi digirin masters ɗaya a fannin ilimi inda ta samu nasara a jarabawar jiha da ta ba ta damar koyar da manyan ɗalibai.
Sai dai a yayin jarabawar neman aiki, ta fuskanci tambayoyi iri daban daban - ɗaya daga cikin waɗanda suka yi jarabawar ta yi mata wata tambaya da ta ɓata mata rai inda aka ce mata ta yaya za a yarda cewa ba za ta rinƙa neman ɗalibai maza ba.
"Na samu nasara a neman ayyukan da na wuce ayyukan ma," in ji ta.
Da aka ɗauke ta aikin daga baya a matsayin malaman koyar da halayyar ɗan adam ta wucin gadi wadda za ta rinƙa koyar da ɗaliban ƙaramar sakandire, ta bayyana cewa ta faɗa wa jami'an makarantar gaskiya
"Na faɗa masa cewa na sauya jinsina kuma na ba shi haƙuri kan jarrabawar neman aikin da na yi. Na yi bayanin kan cewa na kasa biyan kuɗin hayar gidana," in ji ta











