Uttar Pradesh: Musulman Indiya na fargabar hare-haren kiyayya

Anwar Ali
Bayanan hoto, Ana zargin an kashe Anwar Ali yayin wata tarzomar da 'yan Hindu suka yi a watan Maris din 2019

Yayin da jihar Uttar Pradesh ke shirin zaben sabuwar gwamnati, hankali ya koma kan al'ummar Musulmin jihar su miliyan 40 da ke rayuwa a wannan jihar da kawunan jama'arta ke rarrabe.

Kirti Dubey ta BBC Hindi ta duba halin da wasu shari'oi hudu da aka yi da ke nuna yadda ake kai wa al'ummar Musulmi hare-haren kiyayya yayin wa'adin mulkin Yogi Adityanath wanda shi ne babban ministan da ke mulkin jihar.

"Yana yawo da wani dan karamin tawul a kafadarsa a kodayaushe. Sun cusa tawul din cikin bakinsa yayin da suke kashe shi," in ji Kamrun Ali yayin da ta ke kuka, tana bayar da labari kisan da aka yi wa mijinta.

Ana tuhumar cewa wasu mabiya addinin Hindu ne suka kashe mijin nata Anwar Ali yayin wata tarzoma da suka yi a watan maris din 2019 yayin da ya yi kokari hana su rusa wani ginin masallacin da ke kusa da gidansa a gundumar Sonbhadra.

'Yan sanda sun kama mutum18 - dukkansu 'yan Hindu, ciki har da kananan yara - suna tuhumarsu da kashe shi, amma an bayar da belinsu cikin watanni bayan mutuwarsa.

Uwargidan Anwar Ali ta ce har yanzu suna jiran a yi musu adalci.

Kisan gilla da furta kalaman kiyayya ga Musulmi sun dade ana yinsu, musamman tun shekarar 2014, shekarar da jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta firaminista Narendra Modi ta lashe zaben ministan jihar.

Masu sukar lamarin na cewa yawancin wadanda ake tuhuma 'yan jam'iyyar ta BJP ne, sai dai jami'an jam'iyyar sun musanta haka. Amma da wuya ka ji sun soki halayyar kai irin wadannan hare-haren.

Shi kansa Mista Modi ya sha suka saboda kin cewa komai da yayi na tsawon makonni bayan da a shekarar 2015, wani gungun 'yan Hindu suka halaka wani Musulmi mai shekara 52 da haihuwa a jihar Uttar Pradesh saboda wai ya ajiye naman Sa a cikin gidansa.

Kisan na 2015 ya gigita jama'a a fadin duniya, sai dai daga wancan lokacin zuwa yanzu, an ci gaba da kai iri wadannan hare-haren kan Musulmi.

Wasu cikin munanan hare-haren da aka kai kan Musulmi sun auku ne a jihar ta Uttar Pradesh, inda wani malamin addinin Hindu Yogi Adityanath ya rika yin kalaman batanci da na kiyayya ga Musulmi, ya zama babban ministan jihar a 2017.

Da wuya a iya sani yawan mutanen da ka hallaka ta wannan hanyar a Uttar Pradesh a kowace shekara - amma a 2017, ofishin da ke tattara bayanai kan manyan laifukan da aka aikata ya hada kan bayanan amma bai wallafa su ba.

Chief Minister of Uttar Pradesh Yogi Adityanath at the release of the Development booklet highlighting development work during four years of his government, at Lok Bhavan on March 19, 2021 in Lucknow, India.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Adityanath ya dade yana tayar da hankula kan kalamansa da ke raba kawuna

Ckin wasu hare-hare hudu da BBC ta gudanar da bincike a kai, 'yan uwa wadanda aka kashe sun ce ba su gamsu da matakan da 'yan sanda ke dauka ba, kuma sun ce hukumomi ba su nuna cewa sun damu da daukan mataki a kan koken nasu ba.

Prashant Kumar wanda jami'in da ke kula da ofishin shari'a na jihar ne ya musanta zargin iyalan cewa 'yan sanda na nuna halin ko-in-kula.

"Babu wanda ke da ikon yi wa wani duka, kuma idan muka kama wani na yin haka, to muna daukan matakin shari'a kansu," inji shi.

Sai dai wai lauya mai suna Mohammed Asad Hayat da ke wakiltar iyalan da aka kai wa hare-haren nuna kiyayya ya ce halin jami'an tsaron ya yi wa binciken da suke yi illa saboda suna gudun bata wa manyan mutane rai.

Ya ce, "an kashe mutane ne a karkashin yanayi na siyasa."

Amma wasu iyalan da kashe-kashen suka shafa sun ce suna rayuwa cikin fargaba, kuma wasunsu ma sun tsere daga gidajensu.

Iyalai na cikin taraddadi

Babban dan Anwar Ali mai suna Ain ul Haq, ya yi ikirari cewa isowar wani malamin makaranta Ravindra Kharwar ya haifar da tashin hankali a kauyensu na Parsoi.

"Ya rika tara matasa mabiya addinin Hindu, yana zuga su da su rika zagin Imam Chowk (wurin da wani ginin adinin Islama yake a da)," iji shi.

Mista Haq ya ce gubgu 'yan Hindun sun lalata wuri sau biyu, amma 'yan sanda su shiga tsakani kuma an sake gina wurin.

Amma ranar 20 ga watan maris na 2019, kamar yadda 'yan sanda suka ce, Ali ya kama wasu matasa 'yan Hindu na kokari rusa ginin a karo na uku, kuma nan take suka kai ma sa hari. Dan nasa ya ce sun kashe shi.

Binciken asibiti kan gawarsa ya ce an kashe shi ne da "wani makami mai kaifi."

Kamrun Ali
Bayanan hoto, Uwargidan Anwar Ali ma suna Kamrun Ali ta ce har yanzu ba a yi musu adalci ba

Binciken 'yan sanda ya gano cewa Mista Kharwar na da hannu a kisan. Sun kai wani samame a gidansa amma ba su same shi ba - kuam 'yan sanda sun ce "ya tsere" ne. Mista Kharwar ya musanta aikata wannan kisan.

Sai dai da 'yan sanda suka shigar da kara, ba a ga sunansa cikin wadanda suke tuhuma ba.

Daya daga cikin wadanda ake tuhumar Rajesh Kharwar ya shaida wa BBC malamin makarantar ya rika gaya mu su cewa Musulmai hatsari ne ga 'yan Hindu.

Kusan shekara uku bayan kisan kan, Mista Haq ya bayana damuwarsa gani cewa an bayar da belin dukkan mutum 18 din da ake tuhuma.

Irin wannan halin ne ke damun Shahrukh Khan, wanda aka kashe mahaifinsa a wata Yunin 2021 a gundumar mathura yayin wata takaddama da wasu kauyawan da "ba a san ko su wane ne su ba", yayin da yake jigilar wasu shanu.

Bayan wata bakwai babu wanda aka kama, sai dai dan nasa ya zargi Chandrashekhar Baba wani malamin addini Hindu da kashe mahaifin na shi. Mista Chandrasekhar ya musanta aikata laifin.

Sher Khan
Bayanan hoto, An harbe Ser Khan har lahira yayin da yake jigilar wasu shanu

Rayuwa cikin fargaba, masu laifi kuma sun tsere

A watan Mayun bara, wani bidiyo da ya yadu kamar wutar daji ya nuna yadda wani gungun maza na dukan wani mutum a gundumar Moradabad, lamarin da ya tayar da hanula a shafukan sada zumunta.

Bayan da BBC ta ziyarci gidan mutumin da aka yi wa duka mai suna Shakir Qureshi, mahaifiyarsa ta fara kuka domin fargaba. Sai dai daga baya ta kyale shi yayi magana.

Mista Qureishi, wanda mahauci ne, ya ce wata rana yana kan hanyarsa ta kai wa wani abokin cinikinsa naman Bauna a bisa babur, sai wasu mutane suka tare hanya kuma suka zarge shi da jigilar naman Sa.

"Na yi kuka kuma na gaya musu cewa ba naman SA nake dauke da shi ba, amma su ci gaba da duka na."

Shakir Qureshi
Bayanan hoto, An yi wa Shakir Qureshi duka yayin da yake kai wa abokin cinikinsa naman Bauna

Ya ce fargabar abin da zai biyo baya ta hana shi kai kara ga 'yan sanda - sai dai ya yi haka ne bayan da bidiyon ya yadu kamar wutar daji.

'Yan sanda sun kama mutum shida, ciki har da Manoj Thakur, wanda ke da alaka da kungiyar 'yan sa kai ta 'yan Hindu. An tsare Mista Thakur na watanni biyu kafi daga baya a ba shi beli.

Sai dai baya harin da aka kai kansa, mista Qureshi ya daina sayar da nama - yanzu yana aiki ne a matsayin lebura.

A watan Mayun 2017, an gano gawar Ghulam Ahmed mai shekara 60 da haihuwa cikin wani gandun da aka shuka mangwaro da yake gadi a kauyensu da ke gundumar Bulandshahr - kuma binciken asibiti kan gawarsa ya nuna cewa ya mutu ne saboda "munanan raukukan da ya samu a cikin jikinsa".

'Yan sanda sun kama mutum tara wadanda ke da alaka da wata kungiya ta masu tsattsauran ra'ayi - Hindu Yuva Vahini - da Mista Adityanath ya kafa a 2002. An bayar da belin dukkansu kuma sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.

Ghulam Ahmed
Bayanan hoto, An kashe Ghulam Ahmed kwanaki kadan bayan da wani makwabcinsa Musulmi ya tsere da wata mata 'yar Hindu

Iyalan Ghulam na cikin tsirarun Musulmi a kauyen da 'yan Hindu suka mamaye.

Amma tuni sun bar kauyen. "Ya za mu ci gaba da zama a wannan kauyen?" in ji iyalan gidan Ghulam Ahmed.