Karnataka: 'Sanya hijabi ba ƙuntata wa matan Musulmi ba ne'

Mata Musulmi sun fusata inda suka fito suna bayyana zaɓinsu na sanya hijabi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata Musulmi sun fusata inda suka fito suna bayyana zaɓinsu na sanya hijabi
    • Marubuci, Daga Zoya Mateen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Delhi

Nabeela Shaikh, tana shekara 30 ta fara sanya hijabi. Ita ce ta ƙarshe cikin ƴan uwanta mata da suka zaɓi hijabi.

Babbarsu, Muzna, ta fara rubutuwa lokacin da take shekara takwas, ƴar uwarta ta ƙarfafa mata guiwa. Ta ci gaba da saka wa amma ya danganta da waɗanda take tare da su - kafin ta fahimci cewa ba ta "burge kowa"

Karamarsu, Sarah girmanta ya kai lokacin da burinta na zama likitar tiyata ya gamu da cikas saboda rashin samun makin da ya kamata a jarabawa. "Ta fara da abubuwa kamar yin sallah da wuri," in ji ta.

Daga baya na koma Hijabi lokacin da ta zama jiki."

Ƴaƴan likitoci biyu, matan 'ƴan uwan juna sun girma ne a birnin Mumbai na India. Mahaifiyarsu har yanzu ba ta rufe kanta. Amma idan suka yi, mutane na tunanin an tilasta masu ne.

Ana sanya hijabi sosai a Indiya, inda nuna addini ba wani sabon abu ba ne - amma a makon da ya gabata, ɗalibai mata a jihar Karnataka sun yi zanga-zanga kan hana masu saka hijabi a cikin aji.

Muzna, Nabeela and Sarah

Asalin hoton, Muzna Shaikh

Bayanan hoto, Muzna, Nabeela da Sarah sun fara saka hijabi a lokaci daban daban

Tambayar - ko mata musulmi suna da ƴancin saka hijabi a aji - batun na kotu. Takaddamar ta haifar da rikici, ta raba ra'ayin makarantu kuma ya hana wasu dalibai mata a Karnataka halartar ajin karatu.

BBC ta zanta da wasu mata Musulmai a sassan Indiya waɗanda suka ce sun fusata kan wannan yanayin da ake muhawara.

"An sha faɗa muna cewa idan muna so a amince da mu, dole sai mun haƙura da addininmu," in ji wata mata da ke Delhi.

Waɗanda suka zaɓi sanya hijabi sun ce zaɓinsu ba lalle saboda addini ba ne. Amma waɗanda suka zaɓi rashin sanya wa sun ce gashinsu ba shi ne zai tantance addininsu ba.

'Ba a ƙuntata min ba'

"Mutane ba za su fahimci yadda wani yake ji ba idan ya sanya mayafi ba," in ji Nabeela tana dariya. Yana rikitar da su, shi ya sa suke yanke hukunci."

Ƙuntatawa, kalma ce da ake alaƙantawa ga matan da ke sanya hijabi - amma yawanci suna nuna cewa rashin la'akari dalilin da ya sa suke haka ba ya tabbatar da ƴanci ko hana yara zuwa makaranta saboda sun ƙi amincewa su cire."

Matasa mata musulmi sun fito saman titi suna zanga-zangar neman haƙƙinsu. Amma kuma kana nuna min cewa waɗannan matan ba su da tunani nasu?" in ji Naq ƴar shekara 27 daga garin Bangalore da ke yankin kudanci.

Sabani kan hijabi ya haddasa zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sabani kan hijabi ya haddasa zanga-zanga

Lokacin da Naq ta yanke shawarar sanya hijabi shekaru biyar da suka gabata, ta ce ta fuskanci "martani na ban mamaki"

"Hijabi na ya fito da tunanin mutane da dama," in ji ta. "Mutane suna min tsaki: ana ƙuntata maki? kina jin zafi? wane irin man kai kike amfani da shi? mutane suna tambaya ta ko da kuwa ina da gashi - suna tunanin ina da kansa."

A wajenta, hijabi wani sabon abu ne - akwai nau'uka da dama da ke tafiya da launi iri iri.

"Mutane na tunanin hijabi ta, bai dace da tufafi na ba ko kwalliya ta ba. Amma ba komi," in ji ta. Idan na shiga ɗaki, ina son mutane su kalle ni su yi tunani, wannan mace musulma ce da ta cika burinta, tana balaguro a duniya kuma da ci gaba."

Wasu matan Musulmi - kamar Wafa Khatheeja Rahman, lauya da ke birnin Mangalore da ke kudanci - ta ce rashin sanya hijabi bai mayar da su baya ba a Musulunci.

"Ban saka ba saboda bai yi daidai da yadda nike ba - kuma babu wanda zai faɗa min na saka," in ji ta. Amma haka kawai, ba wanda zai kada na saka."

Mata da yawa sun ce suna fuskantar wariya a makaranta saboda sanya hijabi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata da yawa sun ce suna fuskantar wariya a makaranta saboda sanya hijabi

Mahaifiyar Wafa ita ma ba ta saka hijabi - amma ta ce ta girma ne cikin musulmi, tana sauraren tarihi ba wai kawai na Annabi ba har da na matan Musulmi.

Matar farko da Annabi ya aura ƴar kasuwa ce, ta biyu kuma ta yi yaƙi saman raƙumi. Don haka da gaske an ƙuntata muna kamar yadda duniya take son mu yi imani da shi? kamar yadda ta yi tambaya.

Mene ne matsalar zama Musulmi?

Akwai lokacin da Falak Abbar ta tsani rufe kanta, muryar da ba a saba ji ba a Varanasi, birnin da ke yankin arewa na masu ra'ayin riƙau.

Amma tana 16 lokacin da ta gana da Malala Yousafzai, ƴar ƙasar Pakistan da ta lashe kyautar nobel a kafar talabijin wadda ta sauya tunaninta.

"Ta rufe kanta, amma kuma tana da ƙarfi faɗa a ji. A lokacin ta ƙarfa min guiwa na fara rufe kai na."

Makarantarta sun yi ƙi amincewa, suna cewa hijab ta ci karo da nau'in tufafin makaranta, wanda riga ce da wando.

Falak ta yi zargin cewa a kwana uku an hana ta shiga ajin karatu - kuma har ta rasa jarabawar biology. Bayan ta nuna fushinta, hukumomin makarantar suka kira iyayenta suka zarge ta da rashin nuna ɗa'a.

"Sun ce, idan na saka hijabi, zai haddasa matsala ba wai ni kaɗai ba har da makarantar domin kowa zai gane cewa ni musulma ce," in ji ta. "Mene ne matsalar zamanka Musulmi.?

Akwai hanyoyi da dama yadda ake saka hijabi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai hanyoyi da dama yadda ake saka hijabi

Amma ta sauka bayan iyayenta sun faɗa mata cewa "kada ta yi wasa da karatunta saboda hijabi."

Khadeeja Mangat, daga jihar Kerela da ke kudanci ita ma ta fuskanta matsalar.

Makarantarta sun hana ta saka hijabi dare ɗaya a 1997 - daga baya aka ɗage haramcin, amma Khadeeja na mamakin abin da zai iya faruwa a Karnataka.

"Komi yana gabanka - kundin tsarin mulki da manufofinsa da kuma muryoyinmu," in ji ta. "Amma duk da haka an sa sai mun kare kanmu kan abin da ya shafi iliminmu."

Yadda mutane suke kallonka abin takaici ne

Yayin da bahasin da kotu ke saurare ya mayar da hankali kan saka hijabi a ajin karatu, Mata Musulmi suna fargabar yadda hukuncin zai yi tasiri a Indiya a zamanin gwamnatin Hindu ta Firaminista Nerandra Modi.

Simeen Ansar, daga Hyderabad da ke kudanci, ta ce an mayar da hijabi a matsayin wata alama da cimma manufar siyasa.

"Na girma tare da mata ƴan Hindu da suke rufe kafafunsu, wani abin da bai dame ni ba kamar maza ƴan Sikh sanye da rawani," in ji ta.

"Idan ana maganar hijabi, mata musulmi ana rage kimarsu. Ni ƴar gargajiya ce kuma ana ƙuntata min idan na saka ɗaya, amma ana ɗaukata ƴar zamani mai ƴanci idan ban saka ba.

Ana sanya hijab a Indiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana sanya hijab a Indiya

Ta ce ita da ƴan uwanta sun fara saka hijabi, amma sun haƙura saboda an ƙi amincewa da tsarinsu.

Yayin da ƴar uwarta ke fuskantar wariya a wurin aiki, Simeen ta ce mutane na kyararta a wuraren da ba su yi tsammanin ganin mace sanye da hijabi ba - kamar wuraren motsa jiki ko wurin shan barasa ko wurin casu.

"Idan ta hana ni hijabi, me ya rage? Suna na har yanzu na Arabiya ne. Zai zama dole sai na sauya sunan kafin a mutunta ni?"