Wasannin Paralympics: An yi adalci da aka dakatar da 'yan wasan Rasha daga shiga gasa saboda siyasa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Hukumar da ke kula da wasannin Olympics na masu nakasa International Paralympic Committee (IPC) ta zama ta baya bayan nan da ta dauki matakan ladabtarwa kan Rasha.
Tun da farko ta amince wa 'yan wasa daga Rasha da kuma Belarus su halarci wasannin na Olympics na hunturu na 2022 da za a fara a birnin Beijing na kasar China, amma kasa da sa'o'i 24 sai ta sauya ra'ayi, inda ta hana su shiga duka wasannin.
A 'yan kwanakin nan, bangaren wasanni na kasar Rasha sun fuskanci fushin hukumomin wasanni na duniya, ciki har da hana 'yan wasan Rasha shiga gasar kwallon kafa ta duniya da FIFA ke shiryawa, da kuma janye gasar tseren mota ta Formula 1 da ake yi a Rasha a kowace shekara.
Duk da cewa 'yan wasa a kungiyoyi na nuna goyon bayansu ga matakan ladabtarwar da ake dauka kan Rasha, tambaya a nan ita ce: Ina adalcin daukar wadannan matakan?
'Matakan da babu adalci'

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin da ke kula da wasannin Olympics na Rasha ya fitar da wata sanarwa ranar 3 ga watan Maris inda ciki take tuhumar hukumar IPC da daukar matakan ladabtarwa kan 'yan wasan kungiyar kasar.
"Wannan hukuncin ya mayar da 'yan wasan Rasha sun zama su ne masu laifi a wannan rikici na siyasa," in ji kwamitin na RPC.
Hukumar kwallon kafa ta Rasha ta ce hana 'yan wasan kasar shiga wasanni "babu adalci" cikinsa kuma ta ce za ta dauki atakan shari'a akan matakin.
'Babu ruwan wasanni da siyasa'

Asalin hoton, Getty Images
Cikin 'yan wasa, akwai tsohon direban mota da ke yin gasar tseren mota ta Formula 1 Daniil Kvyat - wanda a hali yanzu ke fafatawa a wata gasar tseren mota - ya aika da wani sakon Tuwita yana cewa dakatar da 'yan wasan ya taka tsarin da aka sani na bai wa kowa damar shiga wasanni komai girman bambancin da ke tsakanin bangarori ko kasashe.
Yayin da hukumar da ke kula da tseren mota da FIA ta kyale 'yan Rasha shiga wasannin da ta ke shiryawa, a wasu kasashen an hana 'yan Rasha halartar wasannin. Dan wasan Rasha daya da ke cikin gasar tseren mota ta F1 ba zai ami damar halartar gasar British GP ba wadda za a yi a watan Yuli saboda reshen hukumar na Birtaniya ya dauki matakin hana shi shiga kasar.
'Babban rashin adalci shi ne mamayar da ake wa Ukraine'

Asalin hoton, Reuters
Dakta Keith Rathbone masanin tarihi ne a Jami'ar Macquarie ta birnin Sydney a kasar Australia, ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar a rika sukar yadda ake hana 'yan wasa shiga wasanni.
"Ba laifin 'yan wasa ba ne na matakan da kasashensu ke dauka, amma ana ladabtar da su kan abubuwan da ba su da iko a kai."
Sai dai ya ce ba za a iya kare 'yan wasa daga tasirin rikice-rikice kamar yaki ba.
"Mamayar da ake yi wa Ukraine rashin adalci ne da ya fi rashin adalcin hana 'yan wasan Rasha halartar wasanni."
Shin matakan ladabtarwa kan 'yan wasa na aiki kuwa?

Asalin hoton, Getty Images
Misalai daga tarihi na cewa matakan tarihi da aka dauka a shekarun baya kan wasu kasashe ba su kawo karshen yake-yake ba, kuma ba su sauya rashin adalcin da ya auku ba.
Afira ta Kudu ta shafe shekaru karkashin takunkuman da suka hana 'yan wasant ashiga wasanni a shekarun mulkin wariyar al'umma har zuwa lokacin da ta kawo karshen matakin a 1991.
Sai kuma hana kasar Yugoslavia shiga gasar kwallon kafa ta maza ta Tarayar Turai a 1992, matakin da bai hana kazamin rikici a yankin Balkans aukuwa ba.
Sai dai Rathborne ya ce matakan ladabtarwan da ake dauka na iya yin wani tasiri kan hukumomin Rasha.
"Wasanni sun kasance wasu abubuwa masu muhimmanci ga Rasha da Shugaba Vladimir Putin," in ji shi.
"Saboda haka matakan da hukumomi da kungiyoyin da ke kula da wasanni ke dauka na sake duba dangantakarsu da Rasha na iya haifar da wani abu mai amfani. Ko da kuwa an dauki matakan cikin makararren lokaci sosai ne."











