Abin da ya sa ɗaliban Afirka ke rububin zuwa Ukraine karatu

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Soraya Ali
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Mamayar Rasha a Ukraine ta janyo kwararar fararen hula da suka hada da dubban dalibai daga kasashen Afirka da Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya.
Ukraine ta kasance gida ga ɗaliban ƙasashen waje sama da 76,000, bisa ga bayanan gwamnati daga 2020.
Kusan kashi ɗaya cikin huɗu na ɗaliban sun fito ne daga Afirka, waɗanda suka fi yawa daga Najeriya, da Maroko da Masar.
Aƙalla ba a kasaru ba Indiya tana da ɗalibai sama da 20,000.
Daliban da ke laƙantar ilimin likitanci, da injiniyanci da kasuwanci ne suka fi yawa a cikin ɗaliban.
Amma, yayin da Rasha ta ƙaddamar da farmaki mafi girma a Turai tun bayan yakin duniya na biyu, dubbansu sun yi gudun hijira, yayin da har yanzu ɗruruwa suka kasa fita, kuma da yawa ba su da tabbas game da makomar karatunsu.
Menene abun jan hankali game da Ukraine ?.
Ukraine ta dade tana jan hankalin ɗalibai, a a iya cewa wannan ya samo asali ne tun zamanin tarayyar Soviet, lokacin da aka aka zuba jari mai yawa a manyan makarantu da kuma fara wani ƙoƙari na jawo hankalin dalibai daga sababbin kasashen Afirka masu zaman kansu.
Yanzu, ana ganin jami'o'in Ukrainian a matsayin wata hanyar shiga kasuwar aiki ta Turai, suna ba da ilimi a farashi mai rahusa, ga kuma sharuɗɗan biza kai tsaye da yiwuwar zama na dindindin.
Patrick Esugunum, wanda ke aiki da wata kungiya da ke taimaka wa daliban Afirka ta Yamma da ke son yin karatu a Ukraine ya ce, "An yadda da digirin Ukraine kuma yana da inganci kwarai'
Ya kara da cewa "Dalibai da yawa da ke karatun ilimin likitanci na son zuwa can saboda suna da kyakkyawan tsari na wuraren kiwon lafiya," in ji shi.
Desmond Chinaza Muokwudo, wani dalibi dan Najeriya da ya zauna a birnin Dnirpo, ya ce Ukraine ta ja hankalinsa, ga sauƙin karatu da kuma sauƙin rayuwa fiye da sauran ƙasashen Turai.
Ana ba da darussa da yawa cikin Ingilishi, amma ɗan shekaru 30 ɗin Desmond yana karantar kwas na farko na harshen Ukrain, kafin ya ci gaba da nazarin dangantakar ƙasa da ƙasa.
Yana magana da BBC ne daga wani masaukin baki a Poland bayan da ya tsere wa yaƙin.
Ina daliban suke yanzu?
Kamar Mista Muokwudo, fiye da dalibai 10,000 na Afirka sun yi nasarar tserewa rikici tare da shiga kasashe makwabta, a cewar EU.
An samu rahotannin cewa dalibai 'yan kasashen waje suna fuskantar wariyar launin fata a kan iyakar Ukraine, inda hotunan bidiyon da suka yaɗu a shafukan sada zumunta suke nuna hakan.
Ana kyautata zaton har yanzu akwai ɗumbin ɗalibai a Ukraine, amma da wuya a iya tabbatar da hakikanin adadinsu.
Wani dalibi dan kasar Indiya ya mutu a lokacin da ya fito waje domin siyan abinci.
Christophe, dalibi dan kasar Kamaru mai shekaru 22, ya yi magana da BBC daga cikin wani gini da ke kudancin birnin Kherson da ke kudancin kasar, wanda sojojin Rasha suka kwace.
"Lokacin da tashin bama-bamai suka fara, sai mu rika shiga cikin wani karamin rami " in ji shi yayin da ake ci gaba da gwabza fada.
Ya ce yanzu an samu kwanciyar hankali amma an hana sama da mutane biyu su kasance tare a waje.
A wani bangare na birnin, Mamady Doumbouya, wani dalibi da ke karantar kimiyyar kwamfuta daga kasar Guinea ya ce: "Ina so in koma kasata, ba za mu iya yin karatu a yaki ba."
Ta yi magana da BBC daga cikin wani gida mai duhu inda ita da abokan karatunta na Gabon, da Senegal, da Kamaru suke neman mafaka.
"Ba ruwa ba wuta'' in ji shi.
Megwamnatoci suke yi don taimakawa?
Ukraine ta dakatar da dukkan jiragen farar hula lokacin da aka fara mamaya a ranar 24 ga Fabrairu.
Gwamnatocin Afirka sun yi ta yunƙurin kwashe 'yan ƙasarsu daga ƙasar, inda wasu ke shirya tashin jiragen da ke komawa gida ga waɗanda ke kan iyaka.
Ghana ita ce kasa ta farko a Afirka da ta karbi bakuncin rukunin dalibanta zuwa gida ranar Talata.
Da yake magana da BBC bayan saukarsa a Accra babban birnin kasar, dalibi Jared Otumfuo Catey ya ce: "Kwanaki kadan da suka wuce, ban san cewa zan zo nan ba a yanzu. Ina godiya da na samu nasarar hakan kuma na yi nasara."
Najeriya ta ce za ta bi sahu tare da bayar da jirage ga masu son dawowa ta Romania, da Hungary, da kuma Poland.
Jakadan Afirka ta Kudu a Ukraine ya shaida wa BBC cewa dole ne ya bar Ukraine domin kare lafiyarsa amma ya yi ta kokari wajen ganin an fitar da 'yan Afirka ta Kudu da sauran baki daga kasar.
Jakadun Afirka ta Kudu da Hungary su ma sun je kan iyakokin don taimakawa mutane su shawo kan lamarin, in ji shi.

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin Ukraine ta samar da wani layin kiran gaggawa ga 'yan Afrika da Asiya da ke son ficewa in ji ministan harkokin wajen ƙasar.
A wani saƙon tuwita Dymytro Keluba, ya ce mahukunta na aiki tukuru don kare 'yan Afrika da 'yan Asiya.
Shin za su iya kammala karatunsu?.
Kasancewa sun zuba kudi da yawa don karatunsu a Ukraine, dalibai da dama sun fadawa BBC cewa suna ci gaba da tunani game da ko su ci gaba da zama ko kuma su koma gida domin kammala karatunsu.
''Na sara ya zan yi yanzu, ba zan iya ci gaba da karatuna ba domin dukkan takarduna na hannun hukumar makarantar da nake.
Ita kuwa Jessica Orakpo, dalibai da ke karatun likitanci tsawon shekara shida a Ukraine ta rasa yadda za ta yi, domin watanni hudu kawai suka rage mata ta kammala karatunta.
A Ukrraine, daliban kasashen waje na da damar iya samun gidan zama a kyauta har zuwa tsawon lokacin da za su kammala karatunsu, amma babu irin wannan dama a sauran ƙasashen nahiyar Turai.













