China: Kasa mai kashe kudi sosai ko babbar mai bayar da basussuka?

Workers produce large building materials and equipment for export to countries along the Belt and Road. Hai 'an city, Jiangsu Province, China, June 15, 2020.

Asalin hoton, Costfoto/Barcroft Media via Getty Images

Bayanan hoto, Injiniyoyi a lardin Jiangsu, na aikin kera kayan aki da za a fitar zuwa kasashen waje ta hanyar Belt and Road ta kasar China
    • Marubuci, Daga Celia Hatton
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Kasar China ta bayar da akalla ninki biyu na kudaden raya kasa kamar Amurka da sauran manyan kasashe, kamar yadda wasu sabbin shaidu suka nuna, inda akasari sun fito ne a yanayin basussuka da ruwa masu yawa da kuma hadari daga bankukan kasar ta China.

Yawan adadin basusussukan da China ke bayarwa na da matukar ban mamaki. Ba da dadewa ba ne kasar ta China ta samu tallafi daga kasashen waje, amma kuma yanzu reshe ya juye da mujiya.

A cikin watanni 18, China ta bayar da bashin dala biliyan 843 na ayyukan gine-gine 13,427 a fadin kasashe 165, kamar yadda AidData, wani dakin bincike na William & Mary a Jami'ar Virginia ta Amurka ya bayyana.

Ana danganta akasarin kudaden da burin ayyukan gine-gine na shugaban kasar China Xi Jinping wato shirin nan na Belt and Road.

An fara gudanar da shi a shekarar 2013, kuma ya bayar da dama wajen kwarewar China a fannin ayyukkan gine-gine da kuma samun kudaden kasar waje na gina sabbin hanyoyin kasuwanci na kasa da kasa.

Amma kuma masu suka na fargabar cewa cin basussuka da ruwa masu yawa da ke tallafa wa ayyukan kasar ta China na kara saka yawan al'ummar kasar cikin matsanancin kangin basusussukan da ba su taba tsammani ba.

Masu bincike daga cibiyar ta AidData da suka shafe shekaru hudu suna bin diddigin duka basussuka da China ke bayarwa a kasashen waje da kuma kudaden da take kashewa- sun bayyana cewa ma'aikatun gwamnatin China tana yawan zuwa wajensu don neman bayanai kan yadda ake amfani da kudaden kasar China a kasashen waje.

"Mu kan ji daga mahukunta a China a ko da yaushe cewa 'ba za mu iya saka hannunmu cikin wadannan bayanai a cikin gida ba," in ji Brad Parks, babban daraktan na AidData.

The Yumo railway from China to Laos under construction in Yuxi, Yunnan, China on 26 May, 2019

Asalin hoton, TPG/Getty

Bayanan hoto, Layukan dogo na Yumo zai hade da na kasashen China da Laos - amma kwararru sun ce Laos za ta sha fama wajen biyan basussuka

A cikin shekaru da dama, 'yan siyasa na mamaki game da gina hanyar layin dogo - da za ta hade da kudu maso yammacin China kai tsaye zuwa Kudu Maso Gabashin Asiya.

Amma kuma, injiniyoyi sun yi gargadin cewa akwai bukatar titin jirgin ya bi ta kan tsaunuka, wanda ke bukatar gwamman gadoji da hanyoyin karkashin kasa.

"Bashin da bankin Eximbank na kasar China wanda za a yi amfani da shi wajen gudanar da aikin ya nuna matukar gaggawar da ake bukata na aikin," in ji Wanjing Kelly Chen, mataimakin farfesan bincike a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Hong Kong.

A cikin watan Satumbar shekarar 2020, lokacin tsakiyar fama da kangin basussuka ne, Laos ta sayar da manyan kadarorinta ga kasar China, ta mika bangaren makamashinta kan dala miliyan 600 don samun saukin biyan daga bankunan China masu bin ta bashin.

Kuma duka wannan ya faru ne kan a fara ayyukan gina layin dogon.

Layukan dogon na Laos su ne mafi hadari da bankunan kasar China suka tallafawa da basussuka - amma duk da haka cibiyar bincike ta AidData ta bayyana cewa har yanzu China ita ce mai bayar da tallafin kudi ta farko ga kasashe matalauta da dama.

Presentational white space

A shekarun baya, ana zargin kasashen yammacin duniya da tsunduma kasashen Afirka cikin kangin basussuka.

Chinese President Xi Jinping delivers his speech during the opening ceremony of the Conference on Dialogue of Asian Civilizations in Beijing in May 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Akasarin basussukan ayyukan raya kasashen na China su ma suna bukatar bayar da jingina wani abu da ba a saba yi ba.

China na bayar da bashi ta hanya daban: a maimakon tallafawa ayyukan gine-gine ta hanyar bayar da bashin kudi daga kasa zuwa wata kasa, kusan duka kudin da take bayarwa a matsayin basussukan bankin kasar ne.

Akasarin basussukan ayyukan raya kasashen na China su ma suna bukatar bayar da jingina wani abu da ba a saba yi ba.

Basussukan kasar China kan bukaci masu karba su yi alkawarin biya daga cikin arzikin ma'adinansu.

Ga misali a wata yarjejeniya da ta yi da kasar Venezuela, ta bukaci masu karbar bashi daga kasar da suka saka kudaden kasar waje da suka samu daga man daga suka sayar kai tsaye zuwa asusun bankin da kasar China ke rike da iko.

Ta haken ne idan aka kasa biyanta bashin sai ta zame daga cikin wadannan kudade da aka saka a cikin asusun.

"Wannan kamar salon ba ni gishiri in ba ka manda ne, suna amfani da shi wajen nunawa masu karbar bashin cewa su ma fa manya ne a nan," kamar yadda Brad Parks ya bayyana.

"Sakonsu shi ne: 'Za ka biya mu kafin kowa saboda mu kadai ne muke tambayar wannan kudi'.

"Kasar China na da wayo kenan? Abin mamaki," in ji Anna Gelpern, wata farfesar shari'a a Georgetown da ke cikin binciken na cibiyar AidData da aka gudanar a cikin wannan shekarar, wanda ya duba yanayin basussukan kwangilolin ayyukan raya kasa na China.

Nan ba da dadewa ba China za ta iya fuskantar gogayyar bayar da basussuka ta kasa da kasa.

A taron kasashe masu karfin arzikin masana'antu na G7 cikin watan Yuni, Amurka da kawayenta sun sanar da cewa taron ya tsaida shawarar tsarin kashe kudade ga China abokiyar goyayyarta, wanda aka yi alkawarin tallafin kasashen duniya na ayyukan gine-gine cewa za su kasance masu dorewa ne a fannin kudi da muhalli.

Amma kuma wannan tsari za a iya cewa ya yi latti.

"Ina wasu-wasi cewa yunkurin kasashen Yamma zai haifar da cikas ga tsare-tsaren China," in ji David Dollar, babban jami'i a Cibiyar Brookings kuma tsohon wakilin Baitulmalin Amurka a China.

Masu binciken na AidData sun gano cewa ayyukan hanya na Belt and Road na fuskantar matsaloli.

Akwai yiwuwar suna da alaka da cin hanci da rashawa, da badakalar ayyukan kwadago ko kuma matsaloli na muhalli fiye da na yarejejeniyar kasuwancin raya kasashe na China.

Kan haka ne masu binciken suka ce muddin ana son bin diddigin ayyukan na BRI dole sai Beijing ta daura damarar shawo kan matsaloli da damuwar masu karbar basussukan.