Su wane ne Musulman Uyghur da ake zargin China na yi wa kisan ƙare-dangi?

Asalin hoton, Getty Images
An zargi China da aikata laifukan cin zarafin bil'adama da kuma yiwuwar kisan ƙare dangi kan al'ummar Uyghur da sauran ƙabilun da galibinsu Musulmai ne a yankin Xinjiang da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi imanin cewa China ta tsare ƴan Uyghur miliyan ɗaya ba tare da son ransu ba a shekarun da suka gabata a cikin wani shiri da ƙasar ta kira "sansanin bayar da ilimi", tare da yanke wa dubbai hukuncin ɗauri a gidan yari.
Haka kuma akwai hujjojin da ke nuna ana tursasa wa ƴan Uyghur yin aikin bauta da kuma yi wa matansu abubuwan da ke hana haihuwa.
Wasu kuma da aka tsare da su ana zargin cewa an azabtar da su da kuma cin zarafinsu ta hanyar lalata.
Amurka na daga cikin cikin ƙasashe da dama da ke zagin China da aikata kisan ƙare dangi a Xinjiang. Manyan ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam biyu Amnesty da Human Rights Watch sun wallafa rahoton da ke zargin China da cin zarafin bil'dama.
China ta musanta dukkanin zarge-zargen da ake mata na cin zarafin ɗan Adam a Xinjiang, tana mai ikirarin cewa shirinta na "ilimi" tsari ne na magance matsalar masu tsattsauran ra'ayi a yankin.

Asalin hoton, Google
Su wane ne Uyghur?
Akwai ƴan Uyghur kimanin miliyan 12, akasarinsu Musulmai, da ke zaune a Xinjiang, wanda a hukumance aka sani da yankin Xinjiang Uyghur (XUAR).
Ƴan Uyghur suna magana ne da harshensu, wanda ke kama da na Turkiyya, kuma suna ganin al'adunsu da kabilarsu ta fi kusanci da ƙasashen yankin Asiya ta tsakiya. Ba su kai rabin yawan mutanen Xinjiang ba.
A shekarun baya ƴan ƙabilar Han na China (masu rinjaye) suka kwarara zuwa yankin Xinjiang, wanda ake zargin gwamnatin China ce ta haifar da kwararar su domin shafe tsirarun ƙabilun yankin.
An kuma zargi China da mayar da hankali kan shugabannin Musulmi tare da hana su gudanar da harakokin addininsu a yankin tare da tarwatsa masallatai.
Masu fafutika na Uyghur na fargabar cewa al'adunsu na fuskantar barazana.

Labarai masu alaƙa

Ina ne Xinjiang?
Xinjiang yana arewa maso yammacin kasar China kuma shi ne yanki mafi girma a kasar. Kamar Tibet, yana da ƴancinsa, ma'ana - a ka'ida - yana da ƙarfin ikonsa. Amma a aikace, yankuna biyu suna fuskantar takura daga gwamnatin China.
Xinjiang yanki ne da ke da yawan hamada kuma yana samar da kusan kashi biyar na auduga a duniya.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana damuwarsu cewa yawancin audugar da ake fitarwa ana samar da ita ne ta hanyar tursasa aikin ƙarfi.
Kuma a shekarar 2021 wasu kamfanonin kasashen yamma suka dakatar da karɓar audugar Xinjiang daga tsarinsu, wanda hakan ya haifar da koma baya ga China da yan kasuwa.
A watan Disamban 2020, wani bincike da BBC ta gani ya nuna mutane kusan rabin miliyan ana tursasa masu aikin auduga a Xinjiang.
Akwai wasu hujjoji da ke nuna cewa an gina masana'antu a cikin sansanin da China ke ikirarin na ilimi ne.
Yankin na da arzikin mai da gas kuma saboda kusancinsa da tsakiyar Asiya da kuma Turai, Beijing na ganin yankin wani mai muhimmanci ne ga kasuwancinta.
A farkon ƙarni na 20, mutanen Uyghur suka ayyana ƴancin gashin kai na yankin amma kuma aka dawo da shi ƙarƙashin ikon gwamnatin kwaminisanci ta China 1949.

Asalin hoton, Getty Images
Wane zargi ne da ake yi wa China?
Ƙasashe da dama da suka hada da Amurka da Canada da Netherlands, sun zargi China da aikata kisan ƙare dangi - wanda wani taron duniya ya bayyana a matsayin "niyyar tarwatsawa, gaba ɗaya ko wani ɓangare na ƙasa ko ƙabila ko launin fata ko addini."
Matakin ya biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa, har ma da kafa sansanoni domin ƴan Uyghurs, China tana amfani da ƙarfi wajen yi wa mata abubuwan da zai hana su haihuwa na nufin ɗakile yawan ƴan ƙabilar, da raba yara da danginsu, da kokarin karya al'adun gargajiya na ƙabilar.
Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken, China tana aikata kisan ƙare dangi da kuma laifukan cin zarafin bil'adama.
Ministan harakokin wajen Birtaniya Dominic Raab, ya ce abin da ake yi wa ƴan ƙabilar Uyghur "keta hakkin ɗan adam ne," kuma majalisar Birtaniya a watan Afirlun 2021 ta ayyana cewa China ta aikata kisan ƙare dangi a Xinjiang.
Wani kwamitin kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a 2018 ya ce yana da hujjoji da ke tabbatar da China tana tsare da mutane kusan miliyan ɗaya a sansanoni a Xinjiang.
Wata cibiyar Australia ta gano wasu hujjoji a 2020 na waɗannan sansanonin sama da 380 a Xinjiang, adadin da ya ƙaru da kashi 40 idan aka kwatanta da ƙiyasin baya.
Wasu bayanai da aka bankaɗo da ake kira kwarmaton China sun tabbatar da cewa an yi sansanonin ne a matsayin manyan gidajen yari masu cike da tsaro domin bayar da horo da azarbtarwa.
Wasu mutane da dama sun gudu daga sansanonin kuma sun bayar da rahoton azabtarwa. Mata sun bayyana yadda ake masu fyade da cin zarafinsu.
Me ya ƙara haifar da wannan?
Masu adawa da kabilar Han ta China da kuma fafutikar a ware sun ƙara ƙaruwa a yankin Xinjiang tun daga 1990, wani lokaci yakan kai ga haddasa rikici.
A 2009 kimanin mutum 200 suka mutu sakamakon rikici a Xinjiang, inda China ta ɗora laifin akan ƴan Uyghur da ke naman kafa ƙasarsu.
Yankin na Xinjiang yanzu haka yana cikin tsauraran matakai na tsaro, da ya ƙunshi rundunar ƴan sanda da shingayen bincike da kyamarori wadanda ke bin komai tun daga lambobin mota zuwa fuskokin mutune.
A cewar kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch, ƴan sanda suna kuma amfani da wata wayar hannu domin lura da halayyar mutane, kamar yawan wutar da suke amfani da ita da kuma yadda suke amfani da kofar gidansu.
Tun 2017 da shugaba Xi Jinping ya kafa wata doka cewa dukkanin addinai a China dole su saje da ɗabiun China, aka ƙara ɗaukar matakai na musgunawa. Masu fafutika sun ce China na son kakkabe al'adun ƴan Uyghur.
Me China ta ce?
China ta musanta dukkan zarge-zargen take hakkin bil adama a yankin Xinjiang.
Ta ce a shekarar 2019 ne ta saki dukkanin waɗanda take tsare da su a shirinta da ta kira "na ilimi", duk da cewa waɗanda abin ya shafa yankin na nuna cewa har yanzu ana tsare da dama kuma an sauya da yawa daga sansanoni zuwa gidajen yari na yau da kullum.
China ta ce murkushewar da ta yi a Xinjiang ya zama dole don daƙile ta'addanci da kuma kawar da tsattsauran ra'ayin Islama kuma sansanonin sun yi tasiri wajen wayar da kan fursunoni a yaƙin da take da ta'addanci.
Ta jaddada cewa mayaƙan Uyghur na da'awar tabbatar da ƴancin gashin kai ta hanyar dasa bom da kuma yin zagon ƙasa da haifar da tashin hankali, amma ana zarginta da da yayata barazanar domin ta tabbatar da matakin da ta ɗauka kan Uyghur daidai ne.
China ta musanta iƙirarin cewa tana neman rage yawan ƴan Uyghur ta hanyar hana matansu haihuwa wanda ta kira "marar tushe," sannan zargin tursasa aikin ƙarfi ƙirƙirarsa aka yi.











