China: BBC ta bankaɗo yadda jami'an tsaron kasar suke yi wa mata Musulmai fyaɗe

GOOLE

Asalin hoton, Google

BBC ta samu muhimman shaidu da ke bayyana yadda ake yi wa mata fyade da azabtarwa a sansanonin killace Musulmai ƴan ƙabilar Uighur.

Matan, wadanda suka ce an tsare su a sansanin tsawon watanni, sun ce ana azabtar da su da ƙarafan lantarki.

Sun kuma bayyana wani abin da ya faru lokacin da aka tilasta wa kimanin fursunoni 100 kallon wata budurwa da jami'an tsaro suka yi wa fyaɗe a gabansu.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin China ta ce ta duƙufa wajen kare 'yancin mata.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam dai sun ce kusan Musulman Uighur 500,000 ne ake tsare da su.

Ita dai China a kullum tana musanta zargin da ake yi mata na gallaza wa Musulman, inda take cewa tana ilmantar da su ne a wasu sansanoni na koyar da sana'o'in hannu domin raba su da aƙidar tsananin kishin addini.

Tursunay Ziawudun spent nine months inside China's network of internment camps
Bayanan hoto, Tursunay Ziawudun ta shafe wata tara a sansanin azabtarwa na China

Yadda ake durfafarsu

Ko da yaushe mutanen kan sanya takunkumi su rufe fuskokinsu in ji Tursunay Ziawudun, duk da cewa a lokacin ma annobar cutar korona ba ta ɓarke ba. Su kan sanya kwat ba kakin ƴan sanda ba, a cewarta.

A wasu lokutan da daddare, su kan je kurkukun don zaɓar matan da suke so su kai su wata ƙurya, wani waje da suke kira "baƙin ɗaki," inda babu kyamarorin da suke ɗaukar abin da ke faruwa.

Ziawudun ta ce sun sha ɗaukarta a wasu dararen. "Wannan shi ne mummunan abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba har abada," in ji ta.

"Ba ma na so maganganun su fito daga bakina."

Tursunay Ziawudun ta shafe wata tara a tsare cikin sansanin da ke yankin Xinjiang mai tsananin tsaro.

Ƙiyasin da aka yi mai zaman kansa ya nuna cewa fiye da mutum miliyan daya maza da mata ake tsare da su a sansanonin, waɗanda China ta ce an kafa su ne don sake "ilimantar da su" ƴan ƙabilar Uighur da wasu tsirarun ƙabilun.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce gwamnatin China a hankali ta ƙwace wa ƴan ƙabilar Uighurs ƴancin addini da na sauran abubuwa, inda suke cuzguna musu da bin diddigin abubuwan da suke yi da tsare su da kuma cire ƙwayayen haihuwarsu.

Tsarin ya samo asali ne daga shugaban ƙasar China Xi Jinping, wanda ya ziyarci Xinjiang a shekarar 2014 a yayin da aka fara samun hare-haren ta'addanci daga ƴan awaren Uighur.

Jim kaɗan bayan hakan sai wasu bayanai suka ɓulla daga kafar yaɗa labaran New York Times, inda ya umarci jami'ai da su mayar da martani ba tare da "jin ƙai ba."

Gwamnatin Amurka a watan da ya gabata ta ce matakan da China ta ɗauka na kisan kiyashi ne.

China ta ce rahotannin tsare mutane da cire musu ƙwayayen haihuwa "ƙarya ne da zargi marar tushe."

Ganau ba sa son yin magana

Gulzira Auelkhan makes tea at home in her village. She was detained for 18 months

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gulzira Auelkhan ma an taɓa tsare ta tsawon wata 18 a sansanin

Ba a faye samun labarai daga wajen shaidu a sansanonin ba, amma wasu da aka taɓa tsarewa a baya da wani mai tsaron wajen sun shaida wa BBC cewa sun ga yadda ake yi wa mata fyaɗe da cin zarafi da azabtar da su.

Tursunay Ziawudun, wacce ta tsere daga Xinjiang bayan da aka sake ta a yanzu kuma take Amurka, ta ce a duk dare sai a fitar da mata daga sansanin, mazan nan masu fuska a rufe sun yi musu fyaɗe.

Ta ce sau uku ana azabtar da ita sannan a yi mata fyaɗe, kuma kowane lokaci maza biyu ko uku ne suke yi mata.

Ziawudun ta yi magana da kafofin yaɗa labarai a baya, amma a lokacin da take Kazakhstan, inda take zaune a can "saboda tsoron mayar da ita China," kamar yadda ta ce.

Ta ce idan har ta sake ta yi magana a kan azabtar da su da ake yi, sannan idan tsautsayi ya sa aka mayar da ita Xinjiang, to azabar da za a yi mata sai ta fi ta baya raɗaɗi. Ga shi kuma tana jin kunyar furta wasu abubuwan, in ji ta.

Mafi yawan ƴan ƙabilar Uighur Musulmai ne ƴan ƙabilar Turkic da yawansu ya kusa kai wa miliyan 11 a Xinjiang da ke arewa maso yammacin China.

Yankin yana iyaka da Kazakhstan, kuma a nan ne ƴan ƙabilar Kazakhs suke. Ziawudun ƴar shekara 42 ƴar Uighur ce. Mijinta kuma ɗan ƙabilar Kazakh ne.

Ma'auratan sun koma Xinjiang a ƙarshen shekarar 2016 bayan da suka shafe shekara biyar suna zaune Kazakhstan, sannan an tuhume su a lokacin da suka isa, aka ƙwace fasfunansu, in ji Ziawudun.

Watanni kaɗan bayan nan ƴan sanda suka umarce ta ta je wani taro ita da sauran ƴan ƙabilun Uighurs da Kazakhs, daga nan sai aka kame su duka aka tsare.

Secret filming obtained by the Bitter Winter activist group showed cells with bars and cameras

Asalin hoton, BITTER WINTER

Bayanan hoto, Yadda sansanin da ake tsare mutanen yake