An yi zanga-zangar goyon bayan Musulmin China

Daruruwan mutane sun yi zanga-zangar nuna goyon baya ga Musulmi 'yan kabilar Uighur a birnin Amsterdam da ke kasar Netherlands a ranar Lahadi.

Masu zanga-zangar sun nuna fargabar samun kansu a irin halin da Musulman Uighur ke ciki.

Asalin hoton, NurPhoto

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun nuna fargabar samun kansu a irin halin da Musulman Uighur ke ciki
Masu zanga-zangar suna kiraye-kirayen nuna goyon baya ga Musulmin China

Asalin hoton, NurPhoto

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun yi ta yin kiraye-kirayen nuna goyon baya ga Musulmin China
Uighur kabila ce mai yawan kusan miliyan 11 da ke zaune a yammacin China da ake kira Xinjiang.

Asalin hoton, NurPhoto

Bayanan hoto, Uighur kabila ce mai yawan kusan miliyan 11 da ke zaune a yammacin China da ake kira Xinjiang
An sha zargin China da tsare 'yan kabilar ba tare da shari'a ba a gidajen yari masu matukar tsaro

Asalin hoton, NurPhoto

Bayanan hoto, An sha zargin China da tsare 'yan kabilar ba tare da shari'a ba a gidajen yari masu tsananin tsaro
Ana zargin China da tilasta wa 'yan kabilar Uighur koyon harshen Mandarin

Asalin hoton, SOPA Images

Bayanan hoto, Ana zargin China da tilasta wa 'yan kabilar Uighur koyon harshen Mandarin
China takan ce "ana ilmantar da 'yan kabilar Uighur ne amma wasu bayanai sun nuna yadda ake azabtar da mutane ta hanyar kulle su da kuma koya masu wani addini na daban.

Asalin hoton, SOPA Images

Bayanan hoto, China ta kan ce "tana ilmantar da 'yan kabilar Uighur ne."
An cire dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil daga cikin wasan bidiyo na kwamfuta na Pro Evolution Soccer 2020 samfurin na China sakamakon sukar da ya yi wa hukumomin China na gallaza wa Musulmin kasar 'yan kabilar Uighur

Asalin hoton, SOPA Images

Bayanan hoto, An cire dan wasan Arsenal Mesut Ozil daga cikin wasan bidiyo na kwamfuta samfurin China sakamakon sukar da ya yi wa hukumomin China kan batun