An kuɓutar da 'yan cirani sama da 500 a tekun Bahar-rum

Asalin hoton, EPA
Jirgin ruwan da ke tsaron gaɓar tekun Italiya ya kuɓutar da 'yan cirani 539 daga wani jirgin ruwan kamun kifi da ya nutse daga tsibirin Lampedusa.
Al'amarin da ya faru ranar Asabar ya sa an kubutar da 'yan cirani da dama, wanda shi ne adadi mafi girma na 'yan cirani da aka wuce da su tsibirin Lampedusa a cikin kwana daya.
Mata da yara na cikin wadanda ke cikin jirgin. Wasu daga cikin 'yan ciranin wadanda ke tafiya ta Tekun Bahar Rum daga Libya suke, kuma rahotani sun ce akwai alamun cin zarafi a jikinsu
Masu gabatar da kara a Italiya sun bude bincike kan abin da ya faru.
Wata likita daga kungiyar agaji ta likitoci watau MSF, Alida Serrachieri, ta ce da yawa daga cikin yan ciranin sun gamu da munanan raunuka a Libya yayin da suke jiran jirgin ruwa da zai kai su Turai.
Masu bincike na duba yiwuwar watakila 'yan ciranin an daure su a gidan yari a Libya, in ji kafofin yada labarai na cikin gida.
Magajin garin tsibirin Toto Martello ya bayyana ceton a matsayin "daya daga cikin manyan ayyuka a 'yan kwanakin nan".
Lampedusa na ɗaya daga cikin manyan wuraren da mutanen da ke son zuwa turai suke bi .
A watan Mayu, 'yan cirani sama da dubu ɗaya ne suka sauka a tsibirin Italiya a cikin 'yan sa'o'i kaɗan.
Tsibirin yana da sansanin 'yan ci -rani wanda asali an tsara shi don ɗaukar mutane ƙasa da 300.
Yanzu adadin ya ninka sau biyar, kuma galibi sun fito ne daga ƙasashen da ba su cancanci mafaka ba.











