BBC Africa Eye: Yadda ƴan ci-ranin Habasha ke tafiyar kilomita 2,000 mai cike da hatsari zuwa Saudiyya
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon:
Duk shekara dubban ‘yan kasar Habasha ne suke tafiya a ƙasa mai hatsari ta kilomita 2,000 daga kasarsu zuwa Saudiyya, inda suke yunkurin tsallaka tsaunuka da hamada da Bahar Maliya da kuma fagen yaki.
Wasu daga cikin wadannan ƴan ci-rani sun bayyana yadda suke haduwa da ‘yan fashi, da masu ƙwace da kuma yunwa a cikin yanayi da zafinsa ya wuce digiri 50.
Ba abin mamaki ba ne yadda da dama daga cikinsu suke mutuwa a kan hanya, yayin da guzirin wasu yake karewa inda suke komawa bara a kan tituna.