Wilder Ladino: Labarin yaro ɗan shekara 2 ɗan ci-rani da aka gani yana gararanba a titin Mexico shi kadai

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Darío Brooks
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
An gano Wilder Ladino García yana tsaye, kusan tsirara a kusa da wata gawa da ke gefen babbar hanya a kudu maso gabashin Mexico.
Yaron mai shekara biyu, ya baro garin Santa Rita da ke kasar Honduras tare da mahaifinsa, Isidro Ladino. A lokacin suna ƙoƙarin shiga Amurka, a wannan tafiyar ne suka rabu da mahaifinsa.
Hukumomin Mexico, da masu gadin iyaka da hukumar shige da fice ne suka gano Walker a ranar 28 ga watan Yuni, a gefen hanya a kusa da birnin Las Choapas, da ke jihar Veracruz.
Sananniyar hanya ce da 'yan ci rani ke bi domin isa Amurka.
Adadin 'yan ci ranin da suke kokarin shiga Amurka ta iyakar Mexico sun karu a dan tsakanin nan, adadin da aka dade ba a gani ba cikin shekara 20 da suka gabata kamar yadda hukumar shige da fice da bayyana.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar hana fasa ƙwaurin Amurka, da masu gadin iya sun tsare 'yan cirani 180,034 a watan Mayu kadai, yawancin su matasa da ba su da auri.
Shi ne adadi mafi girma tun watan Afirilu shekarar 2000, an kuma samu karuwar daga Afirka.
A watan Afirilu ma an tsare 'yan ci rani 19,000, yawancinsu yara ƙanana da ba sa tare da iyaye ko 'yan uwansu.
Balaguro cikin a bayan a kori-kurar mara tsafta
Hukumomi sun ce, Wilder Ladino sun yi balaguro tare da 'yan ci rani 100, a bayan wata a kori-kura mai tarin shirgi da datti.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce 'yan ci ranin sun galabaita da rashin abinci da ruwan sha sannan babu isasshiyar iska a cikin motar.
"Abin takaicin, an gano gawar wani matashi dan shekara 25 a cikin a kori-kurar," in ji sanarwar.
Mahaifiya Wilder, Lorena García, ta yi wa BBC ƙarin haske kan abin da ya faru.
Ta ce ta kadu matuka da samun labarin, ta yi farin ciki da aka shaida mata an gano mijin ta cikin koshin lafiya, duk da cewa ba a san takamaimai abin da ya raba shi da ɗan nasa ba.

Asalin hoton, Reuters
Mis García ta yi roƙon a bar uba da ɗan su shiga Amurka.
"Ku taimake ni, ku bar mijina da ɗana su shiga Amurka tare. Kar a raba su, idan haka ta faru zai yi wahala ya sake dawowa gare ni," in ji Garcia tana kuka.
Gujewa talauci
Isidro Ladino ya yanke shawarar yin balaguron tare da ɗansa a ranar 25 ga watan Yuni. Shi da matarsa sun samu jita-jitar idan dan ci rani ya tafi da yaro ana bari ya shiga Amurka.
"Mun ga mutane da dama da suka wuce tare da 'ya'yansu," in ji Mis García.
Sun bar garin Santa Rita, da ke arewacin Honduras - yanki mai cike da tarihi da talauci da guguwar Eta da Iota suka daidaita a shekarar 2020.
"Babu abin da ake samu a nan, idan Isidro ya samu aiki shi ne ya kan samu dala huɗu a rana. To aikin ma ba kullum ake samu ba, ba shi da taƙamaimiyar sana'a."
A ranar 27 ga watan Yuni ne suka yi nasarar tsallaka iyakar kasar da Guatemala.
Mis García ta ce tun daga wannan lokacin ne ba ta ƙara jin duriyar mijin nata da ɗanta ba. Sai daga bisani ofishin jakadancin Hunduros ya tuntuɓe ta, tare da ba ta labarin abin da ya faru, kan cewa an tsinci ɗanta shi kadai a kan titi yana gararanba.
Duk da cewa ta yi magana da mijinta ta wayar tarho, Mis García ta ce har yanzu ba ta san abin da ya raba Ladino da ɗansu ba.
"Ban san abin da ya raba su ba. "
Hukumomin Mexico sun samu bayanin balaguron da 'yan ci ranin suka yi mai cike da wahala da galabaita, sakamakon yadda suke tafiya a cunkushe a motar daukar kayan da babu isasshiyar iska ga kuma tarin ƙazanta.
Hukumar shige da ficen Mexico ta ce, "Ƴan ciranin sun shaida mana yadda abokan tafiyarsu ke yanke jiki su fadi, sakamakon tsananin zafi da rashin iskar shaƙa."

Asalin hoton, Reuters
Sun kuɓuta, amma sun rabu
Sai a ranar 29 ga watan Yuni Lorena García ta samu labarin mijinta da ɗanta suna cikin ƙoshin lafiya.
"Sun shaida min Wilder na cikin ƙoshin lafiya, amma dole za su kai shi ga likitan ƙwaƙwalwa ya duba shi.
Game da mijinta kuwa, an shaida mata yana sansanin 'yan ci rani da ke birnin Tuxtla Gutiérrez na Mexico.
"Ba mu yi wata doguwar magana ba, saboda ba sa bari ya bugo waya akai-akai, amma lafiyarsa ƙalau."
Hukumar 'yan ci ranin ta ce "Matar ta rubuto mana saƙo a ranar 30 ga watan Yuni, sai dai ko an mata saƙo ba ta amsawa."
Duk da hakan dai Mis García, na roƙon hukumomi su taimaka a bari su shiga Amurka, domin Ladino ya samu aikin yi.
"Ina fatan za a taimaka min su shiga Amurka tare."










