Jikokin bayin da aka hana su auren wadanda suke so a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Adaobi Tricia Nwaubani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Nigeria
Abin takaici da yayi kama da hikayar nan ta marubuci Shakespeare ta Romeo and Juliet, wasu masoya biyu sun kashe kansu a farkon wanna watan bayan da iyayensu suka haramta mu su auren juna saboda ɗayansu jikan bayi ne.
"Suna cewa ba za mu iya auren juna ba... kawai saboda wata tsohuwar al'ada," kamr yadda suka rubuta a wata takardar da suka bari.
Masoyan da shekarunsu na haihuwa talatin da wani abu ne, 'yan asalin yankin Okija ne da ke kudu maso gabshin jihar Anmabra, inda turawan mulkin malllak suka han bautar da mutane a farko shekarun 1900.
Amma jikokin bayin da aka 'yantar cikin ƙabilar ta Igbo har zuwa yau na gadon matsayin kakanin nasu na bauta, kuma ala'adu sun haramta mu su auren waɗanda ake kallo a matsayin masu cikakken 'yanci.
"Ubangiji ne ya halicci kowa bisa daidaito, saboda haka, me yasa wasu ke nuna bambanci saboda jahilcin kakanninmu?" inji mamatan.

Akwai 'yan ƙabilar Igbo da ke fuskantar irin wannan wariyar.
Shekara uku da ta gabata, Favour wata mata mai shekara 35 da haihuwa, wadda kuma ba ta bukatar a bayyana sunan mahaifinta na shirin auren wani mutum da ta shafe shekara biyar suna souyayya, sai kawai 'yan uwansa 'yan Igbo suka gano cewa ita jikar bayi ce.
"Sai suka sanar da ɗn nasu cewa ba sa buƙatar ya aure ni," inji Favour, wadda ita ma Igbo ce.
Da farko masoyin nata ya nuna turjiya kan batun, amma matsin lambar da ya fuskanta daga iyayensa da 'yan uwansa sun kawo ƙarshen soyayyarsu.
"Na yi takaicin lamarin. An raunata ni. Na ji zafin abin," inji ta.
Ga arziki ga ƙasƙanci
Ba aure kawai ƙalubalen da jikokin bayin ke fuskanta ba.
Ana kuma hana su shugabanci irin na gargajiya da shiga manyan ƙungiyoyi da tsayawa takarar muƙaman siyasa da wakiltar al'umominsu a majalisa.

Asalin hoton, Adaobi Tricia Nwaubani
Sai dai ba a hana su neman ilimi da samun ɗaukaka a fagen kasuwanci.
Wariyar da aka riƙa nuna mus us ne ya sa yawancinsu suka riƙa shiga addinin Kirista da rungumar ilimin boko da 'yan mishin suka zo da shi a lokacin da sauran 'yan ƙabilar tasu ke nesa-nesa da batun.
Wasu jikokin bayin yankin sun zama manyan attajirai cikin al'umominsu, amma duk da wannan ɗaukakar ana kallonsu a matsayin ƙasaƙantattu.
A shekarar 2017, wata mata mai shekara 44 da haihuwa mai suna Oge Maduagwu ta kafa wata gidauniya mai son kankare al'adun gargajiya da kan sa a kyamaci wasu a al'umarmu (Ifetacsios).
Kuma ta shafe shekara uku da ta gabata tana zaga jihohi biyar na kudu masi gabashin Najeriya domin ilimantar da mutane cewa jikokin wadanda aka bautar na da yanci da daraja kamar kowa.
Ta ce "Jikokin wadanda aka bautar a da na fuskantar bambanci irin wadanda bakar fatan Amurka ke fuskanta a yau."
Ms Maduagwu ba jikar bayi ba ce, amma iat ma ta fuskanci bambanci yayin da ta ke taswa a jihar Imo, abin da ya zaburar da ita - ta far daukar mataki bayan da ta ga batun ya lalata rayuwar wata shaƙiƙiyarta da aka hana auren wani jikan bayi.

Yankin ƙabilar Igbo a Najeriya:


Sai dai irin wannan nuna bambancin ko wariya ba a samunsa tsakanin ƙabilun Yarabawa da Hausawa, waɗanda tare da Igbo su ne manyan ƙabilu uku mafi girma a Najeriya. Amma ana samun irin wannan al'adar a wasu ƙabilun da ke Mali da Senegal.

Asalin hoton, Oge Maduagwu
Gidauniyar Ifetacsios ta Ms Maduagwu na da ma'aikata huɗu da kuma 'yan-sa-kai dozin guda. Aikin mai wahala ne kuma mai cin lokaci, amma akwai wasu shugabannin gargajiya da suka fara rungumar soke al'adun da ke haifar da rashin daidaito a tsakanin al'umominsu.
Ta ce da farko an rika sukar ta a shafukan sada zumunta daga waɗanda ke adawa da aikin da ta ke yi na fafutukar kare hakkin waɗanda ake nuna wa wariya.
"Sai da na riƙa shiga ƙungiyoyin ƙabilar Igbo masu yawa domin in yaɗa saƙon, kuma wasu masu yawa cikinsu sun riƙa zagi na, kuma sun ce min al'adunsu ba za su bace ba."
Adaobi Tricia Nwaubani 'yar jarida ce kuma marubuciya da ke zaune a Abuja.











