Cinikin bayi: Yadda cinikin ya shafi Arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Cinikin bayi wani lamari ne mai ɗumbin tarihi wanda ya samo asali shekaru aru-aru.
A duk lokacin da ɓakar fata suka tuna da yanayin da kaka kakanninsu suka shiga a zamanin cinikin bayi, akasarin su suna fuskantar ɓacin rai.
An shafe sama da shekaru 400 ana gudanar da cinikin bayi inda akasarin bayin ana ɗibarsu ne daga nahiyar Afrika a tafi da su sauran nahiyoyi musamman yankin Amurka da Turai.
Najeriya na daga cikin ƙasashen yammacin Afrika da ke da guraren da aka mayar cibiyoyin hada-hadar bayi kamar Badagry da ke wajen birnin Legas a wancan lokaci.
Kasashen Sifaniya da Portugal da Birtaniya da kuma Faransa ne dai kan gaba a wannan harka ta cinikin bayi.
Duk da cewa babu wata sahihiyar ƙididdiga da za ta nuna adadin bayin da aka kwasa daga nahiyar Afrika zuwa sauran ƙasashe, sai dai an yi ƙiyasin cewa an kwashi sama da mutum miliyan 12 a tsawon shekarun da aka ɗauka ana cinikin bayin.

Asalin hoton, Getty Images
Saboda muhimmancin wannan lamari ne ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware duk ranar 23 ga watan Agustan kowacce shekara domin yin waiwaye kan wannan batu.
BBC ta tattauna da Dakta Babangida Jibril, masanin tarihi da ke koyarwa a kwalejin horar da sojoji ta NDA da ke Kaduna inda ya yi mana bayani kan tasirin da cinikin bayi ya yi ga ci gaban arewacin Najeriya da kuma nahiyar Afrika.
A cewarsa, a lokacin da Turawa suka je Afrika, sun yi amfani da wata hikima da ake kira "trans-atlantic slave trade", wato wani nau'i ne na cinikin bayi da Turawan ke yi inda suke zuwa Afrika su sayi bayi, sai su ɗauke su cikin jirgin ruwa sa'annan sai a kai su yankin Amurka, daga can idan suka yi noman rake, za a ɗauki sikarin da aka yi da raken zuwa nahiyar Turai.
Sai su yi amfani da kuɗin da suka samu daga sikarin da suka siyar kuma sai su sake dawowa Afrika su sayi wasu bayin.

Asalin hoton, Getty Images
Ya ce cinikin bayi ya shafi arewacin Najeriya da nahiyar Afrika gaba ɗaya, inda ya ce "a lokacin ana yawan yaƙe-yaƙe tsakanin garuruwan da ke arewacin Najeriya, idan aka kama bayi, akwai dillalai da suke ɗaukan bayin, za su kai su har bakin Kogin Atlantic, inda daga nan kuma ake ɗaukar su domin tafiya Amurka.
"Shekarun da aka ɗauka ana cinikin bayi a nahiyar Afrika na daga cikin abin da ya sa nahiyar ta zama koma baya wajen ci gaban tatalin arziƙi da na ilimi da ƙere-ƙere," in ji Dakta Babangida.
"Lokacin da nahiyar Turai ta ƙara samun ci gaba na ilimi sai ya zamana wani yanayi na tattalin arziƙi ya shigo wanda ake ce wa Industrial Revolution, wanda wani yanayi ne na amfani da kayan ƙere-kere, wanda wannan ya ja 'yan kasuwa na nahiyar Turai ya zamana ba su buƙatar bayi, hakan ya sa aka bar cinikin bayi," in ji shi
Masana na ganin cewa bayin da aka kwasa zuwa nahiyar Turai da Amurka, an yi amfani da su wurin gina tattalin arziƙin nahiyoyin, inda akasari bayin na aiki tun daga safe har dare a gonaki da masana'antu.
Ruɗun da aka shiga a nahiyar Afrika a lokacin, ya hana jama'ar yankin natsuwa su yi tunanin ci gaban kansu sakamakon fargaba da ake ciki a kullum.
Bugu da ƙari kuma matasa majiya karfi da ya kamata a ce sun tsaya nahiyar ta Afrika an more su, su ne aka rinƙa kwashewa zuwa sauran ƙasashe domin aikin bauta.











