Yadda ake cinikin 'bayi' ta shafukan intanet

Bayanan bidiyo, Ana sayar da dubban mata a matsayin masu aikatau a intanet

Lasta alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Idan mutum ya yi yawo cikin garin Kuwait, ba zai ga irin wadannan matan ana yawo da su ana sayar da su kan tituna ba.

Suna nan kulle cikin gida, an tauye musu hakkinsu, ba za su iya fita ba, kuma a ko da yaushe akwai yiwuwar cewa za a iya sayar da su ga wanda ya fi tayawa da tsada.

Amma idan mutum ya dauki wayar salula, zai iya ganin dubban hotunansu, inda aka kasa su bisa yaruka daban-daban da launin fata inda ake sayar da su kan 'yan dubban daloli.

Wani binciken kwakwaf da sashen BBC na Larabci ya gudanar ya gano cewa ana saye da sayar da masu aikatau ta intanet a kasuwar bayan fage.

Wasu daga cikin cinikayyar da aka yi an yi su ne a shafin Instagram mallakar Facebook, inda ake kwarmata kasuwar ta hanyar amfani da mau'du'i dauke da ''hashtag'' inda idan mutum ya ga yana bukatar masu aikatau din akan tattauna ta hanyar aika sako na sirri wato ''private message.''

Ana kuma amfani da wasu manhajojin wadanda kasuwar sayar da manhajoji ta Google Play da Apple Store suka amince da su domin kara tallata wannan cinikayyar.

Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai bayar da rahoto kan cinikin bayi na zamani Urmila Bhoola ta shaida cewa ''Wadannan manhajojin suna tallata cinikin bayi.

''Idan Google da Apple da Facebook ko wani kamfani yana bayar da damar amfani da irin wadannan manhajoji, dole ne a hukunta su.''

Kamfanin Facebook ya bayyana cewa bayan ya samu labarin irin wannan lamarin, ya dakatar da irin wannan mau'du'in guda daya.

Kamfanonin Google da na Apple sun bayyana cewa suna aiki tare da masu kirkirar manhajoji domin kare yin irin wadannan munanan ayyukan.

Irin wadannan ayyukan sun saba dokar da Amurka ta kafa kan masu kirkirar manhajoji da kuma masu amfani da su.

Sai dai BBC ta gano cewa har yanzu akwai irin wannan cinikayyar da ake yi a shafin Instagram da kuma wasu mahajoji da ake samu daga kasuwar Apple da kuma Google.

Kasuwar bayi

Kashi 9 cikin 10 na gidajen da ke Kuwait suna da masu aikatau - masu aikatau din sun fito daga gidaje da suka fi talauci daga sassan duniya da kuma yankin Gulf inda suke da niyyar yin kudi domin tallafa wa iyalansu.

Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Urmila Bhoola
Bayanan hoto, Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Urmila Bhoola

Masu binciken kwakwaf na BBC sun yi badda kama a matsayin sabon aure ma'ana amarya da ango a lokacin da suka shiga Kuwait. Sun tattauna da masu amfani da manhajar kusan 57 kuma sun ziyarci gwamman mutanen da ake son sayar da masu aikatau wadanda ke amfani da manhajar 4sale.

Akasarin masu sayar da matan 'yan aikatau din, sun kwace fasfo-fasfo din matan, suna kulle su cikin gida, ba su bayar da hutu a garesu kuma ba su barinsu amfani da wayar tarho.

Manhajar ta 4sale tana bayar da dama ga mai son sayen masu aikatau ko kuma bayi tantance wadanda suke son saye ta bangaren launin fata, ko yare, ko shekaru, kuma ko wane rukuni da kudinsa.

A lokacin da masu binciken na BBC suke tattaunawa da wasu masu sayar da bayin, sun ji suna amfani da wasu kalamai munana na wariyar launin fata inda suke cewa '''yan kasar Indiya sun fi kazanta.''

Take hakkin bil adama

Masu son sayar da matan a matsayin bayi sun nemi wakilan BBC da suka yi badda kama da su hana matan da za su saya duk wata dama da bil adama yake da ita ta hutu ko da kuwa hutun minti daya ne.

Wani dan sanda da ya zo sayar da daya daga cikin bayinsa ya shaida cewa: ''Tana da kirki matuka, tana dariya da murmushi a koda yaushe. Ko da kuwa ta kai karfe biyar na asuba tana aiki ba za ta yi korafi ba.

Ya shaida wa BBC yadda ake amfani da masu aikatau a matsayin kayan saye da sayarwa.

''Za ku ga wani ya saya baiwa kan dala 2000 ya siyar da ita kan dala 3,300.''

Sahen BBC na larabci ya nadi sautukan tattaunawa da aka yi da masu cinikin bayi a Kuwait
Bayanan hoto, Sahen BBC na Larabci ya nadi sautukan tattaunawa da aka yi da masu cinikin bayi a Kuwait

Wannan cinikin bayi na zamani ba ana yin sa ne a Kuwait kadai ba.

Binciken ya nuna cewa akwai daruruwan mata da ake sayarwa a manhajar Haraj a kasar Saudiyya. Akwai kuma wasu daruruwa a manhajar Instagram.

A lokacin da ake cinikin Fatou 'yar shekara 16 (ba sunanta na ainahi ba) tare da mai sayar ta ita.
Bayanan hoto, A lokacin da ake cinikin Fatou 'yar shekara 16 (ba sunanta na ainahi ba) tare da mai sayar ta ita.

Mummunan wuri

Masu binciken kwakwaf na BBC sun yi tafiya zuwa kasar Guinea domin kokarin samun tattaunawa da iyayen Fatou, yarinyar da suka gano ana son siyar da ita a Kuwait.

A duk shekara, ana safarar daruruwan matan daga nan zuwa yankin na Gulf.

''Kuwait akwai mummunan bala'i,'' inji daya daga cikin wata da ta taba aikatau da ta bayyana cewa an taba sa ta kwana garke daya da shanu. ''Gidajen Kuwait abin ba kyau,'' inji wata daban kuma. ''Ba bacci babu abinci ba komai.''

Jami'an kasar Kuwait ne suka gano Fatou suka mayar da ita kasar Guinea sakamakon ta yi karama.

Ta shaida wa BBC irin wahalar da ta sha a aikace-aikacen da ta yi a gidaje har uku cikin watanni tara a Kuwait. ''Suna yawan yi mani ihu suna kirana dabba. Abin ya bani haushi, ya bata mani rai amma babu yadda zan yi.''

Amma a yanzu ta koma makaranta a garin Conakry inda BBC ta kai mata ziyara.

BBC ta bi Fatou har gidansu da ke Conakry
Bayanan hoto, BBC ta bi Fatou har gidansu da ke Conakry

''Na ji dadi sosai,'' in ji ta.

''Ko a yanzu da nake baku labari. ina cikin farin ciki. Rayuwata ta sauya a yanzu. Ina ji kamar na fita daga wani kangi na bauta.''