Sudan, Ƙasar Afirkan da ake kiran baƙaƙen fata bayi

Reem Khougli and Issam Abdulraheem

Asalin hoton, Ali al-Nayer

Bayanan hoto, Reem Khougli da Issam Abdulraheem sun fuskanci cin zarafi saboda auren juna da suka yi

A jerin rahotanninmu kan wasiƙu daga 'yan jaridar Afirka, Zeinab Mohammed Salih ta rubuto game da cin fuska mai tayar da hankali a kan wariyar launin fata da ake nuna wa baƙaƙe a Sudan.

Gargaɗi: Wannan maƙala na ƙunshe da kalamai marasa daɗi

Yayin da zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata ta ɓarke a sassan duniya bayan mutuwar Ba'amurke ɗan asalin Afirka George Floyd a hannun 'yan sandan Amurka, Sudan ga alama tana can wata duniya ce ta daban.

Mutane 'yan ƙalilan ne suka damu da taken #BlackLivesMatter wato ''BaƙaƙeSuMaMutaneNe'' a Sudan.

Maimakon bin sahu, masu amfani da shafukan sada zumunta da yawa a Sudan sun riƙa jefa maganganun tozartawa na wariyar launi ga wani fitaccen baƙar fata ɗan ƙwallon ƙafan Sudan, Issam Abdulraheem, shi da wata farar Balarabiya mai sana'ar kwalliya, Reem Khougli, bayan ɗaura aurensu.

"Wai da gaske 'yan mata, wannan ai an aikata haramci... sarauniya ta auri bawanta," wani mutum ya yi sharhi a shafin Fezbuk bayan ganin hoton ma'auratan.

Bidiyon Fezbuk kai tsaye lokacin hutun cin amarci

An samu gomman irin wannan furuci - ba abin mamaki ba ne a ƙasar, da 'yan Sudan da dama ke kallon kansu a matsayin Larabawa, saɓanin 'yan Afirka, sau da yawa a kan yi amfani da kalmar "bawa", da kuma sauran kalaman aibatawa don bayyana baƙaƙen fata.

Fararen fata ne ko da yaushe suka yi babakere a Sudan, su ne manyan gari da ke magana da harshen Larabci, yayin da baƙaƙe 'yan Afirka a kudanci da yammacin ƙasar ke fuskantar wariya kuma ana mayar da su gefe.

Abu ne ruwan dare jaridu su wallafa ɓatanci na wariyar launi, ciki har da kalmar "bawa".

Engraving depicting Abyssinian slaves being taken from the Sudan across the desert to the Red Sea to be taken to Jeddah

Asalin hoton, Universal History Archive

Bayanan hoto, Sudan na daga cikin manyan yankunan cinikin bayi a karni na 19

A 'yan makwannin da suka wuce, wani mai rubuta sharhi kan al'amuran Musulunci a Al-Intibaha, wata jarida da ke fita kullum-kullum mai goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir, wanda bai yarda da ra'ayin mata su buga ƙwallon ƙafa ba, ya bayyana mace kocin Gunners, wata fitacciyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta 'yan mata a matsayin baiwa.

Kuma kusan ɗaukacin kafofin yaɗa labarai na bayyana masu aikata 'yan ƙananan laifuka a babban birnin Khartoum, a matsayin "baƙaƙen fata" don kuwa su ne ake gani matalauta kuma ba Larabawa ba.

Da na tambayi Abdulraheem ko me zai ce game da cin fuskar wariyar launin da aka nuna masa da kuma amaryarsa, sai ya ce: "Na kasa wallafa ƙarin wasu hotuna a shafukana na sada zumunta saboda tsoron ƙarin [zagi]."

Maimakon haka, sai angon ɗan shekara 29 da amaryarsa mai shekara 24 suka yi bidiyon Fezbuk kai tsaye a lokacin hutun cin amarcinsu, inda suka ce suna ƙaunar juna kuma launukan fatarsu ba shi ne mafi fa'ida ba.

Fuskokin baƙaƙen fata kaɗan

A wani abun kuma da ya faru kwanan nan, shugabar wata ƙungiyar kare 'yancin mata, mai suna ''No To Women Oppression,'' ta yi sharhi kan wani hoto da ke nuna wani matashi baƙar fata da matarsa farar Baturiya.

Tana cewa matar, da wannan zaɓen miji da ta yi, mai yiwuwa wani yunƙuri ne na gano halittar da ta ɓace a jerin salsalar da ke tsakanin birran da suka rikiɗe zuwa mutane.

Bayan koke-koken nuna ɓacin rai, Ihsan Fagiri ta sanar da ajiye aiki, amma ƙungiyar No To Women Oppression ƙememe ta ƙi amincewa, tana cewa ba abin da take nufi kenan ba.

A Sudanese protester holds up a sign reading in Arabic "our martyrs are not dead, they are alive with the revolutionaries" along with the English slogans "#BLUEforSUDAN" and "#BLACKLIVESMATTER", as demonstrators mark the first anniversary of a raid on an anti-government sit-in and some demonstrate in support of US protesters over the death of George Floyd, in the Riyadh district in the east of the capital Khartoum on June 3, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dan sha samun zanga-zanga kanana na adawa da wariyar launin fata a Sudan

Wariyar launin fata mugun abu ne a Sudan a tarihi kuma tun bayan samun 'yancin kai, a yayin da mafi yawan masu manyan mukamai suka kasance daga arewacin kasar ne - daga cikin Larabawa dakuma 'yan kabilar Nubiya.

Kusan dukkan manyan jami'an soji sun fito ne daga wadannan al'ummu, wanda hakan ya ba su damar amfani da karfin ikonsu wajen mamaye bangaren kasuwanci.

Map

A yau idan kuka je duk wani sashen na gwamnati ko banki a Khartoum, da wuya ka ga bakin mutum a wani mukami mai muhimmanci.

Sudan ta zamo daya daga cikin matattarar da ake cinikin bayi a Afirka, inda ake daukar bayi daga nan an kai su kudanci da arewacin kasar sai a wuce da su zuwa Masar sai Gabas ta tsakiya sannan a wuce da su zuwa yankin Mediterranean.

Al-Zubair Pasha Rahma babban mai cinikin bayi ne

Asalin hoton, DEA / BIBLIOTECA AMBROSIANA

Bayanan hoto, Al-Zubair Pasha Rahma babban mai cinikin bayi ne

Ana ganin cewa har yanzu ana girmama masu cinikin bayi, inda akan sa sunansu a hanyoyin babban birnin kasar kamar al-Zubair Pasha Rahma.

Masana tarihi sun ce ya kan kama mata a Sudan da ma wuraren da ke mwakbataka da Sudan din.

Sannan kuma yana da dakarunsa da kan taimaka masa wajen kama mutane su mayar da su bayi.

Akwai kuma wani titi da aka sanya wa sunan Osman Digna, wani mai cinikin bayi kuma soja.

A shekarar 1924, aka haramta cinikin bayi a hukumance, amma kuma matakin ya sha suka daga bangaren Larabawa saboda yawanci su akan kai wa bayi su yi wa aiki a gonakinsu.

Zeinab Mohammed Salih
BBC
The superiority complex of many Arabs lies at the heart of some of the worst conflicts in Sudan"
Zeinab Mohammed Salih
Sudanese journalist

Sun rubutawa turawan da ke mulki a lokacin wasika inda suka bukace su da kada a dakatar da cinikin bayi, amma kuma sai aka yi watsi da bukatarsu.

Sudan dai ta jima tana cinikin bayi, inda da kyar abin ya sauya.