Coronavirus: Wadanne labaran karya ne ke yawo a Afirka?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga sashen binciken kwaf na BBC
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Kasashen Afirka na kara samun bullar cutar coronavirus, gwamnatoci da dama na saka dokar bayar da tazara a yunkurinsu na dakile yaduwar cutar.
A daidai lokacin da jama'a da dama ke kara kamuwa da cutar, akwai labarai da dama na bogi da ke yawo a fadin nahiyar.
1. Ba za a yi gwajin riga-kafi kan 'yan Afirka ba
Akwai labarai da dama da ke yawo kan cewa za a yi amfani da 'yan nahiyar Afirka a matsayin zakaran gwajin dafi wurin gwajin riga-kafin cutar coronavirus.
Amma wadannan labaran ba gaskiya ba ne - Har yanzu babu riga-kafin Covid-19 kuma har yanzu gwaji kadan aka yi a asibitoci kan riga-kafin kuma duka ba a nahiyar Afirka ba ne.
Babu tabbacin inda aka samu wadannan labaran, amma labaran na da zummar mayar da hankali kan yadda za a yi amfani da 'yan nahiyar Afirka domin yin gwajin riga-kafin, idan an ga komai ya yi lafiya kalau sai a yi hakan a sauran manyan kasashen duniya.
Daya daga cikin irin wadannan labaran shi ne na wata mata da aka wallafa a shafin Youtube da ta ke magana da Faransanci inda take cewa: ''Akwai riga-kafi da aka tanadar da za a yi wa duka 'yan kasashen Afirka amma babu na kasashen Yamma, ina kira ga 'yan uwana maza da mata na Afirka da kada su yi amfani da wannan riga-kafin.
A yanzu haka wannan bidiyon mutum sama da 20,000 sun kalle shi, kuma mutane da dama na tofa albarkacin bakinsu a shafin inda suke goyon bayanta."



2. Bakar fata na iya kamuwa da Covid-19
Akwai maganganu da dama da ake yi a shafukan sada zumunta inda ake cewa bakaken fata ba su iya kamuwa da coronavirus.
A ranar 13 ga watan Maris, ministan lafiya na kasar Kenya ya yi watsi da jita-jitar da ake cewa ''bakaken fata ba za su iya kamuwa da coronavirus ba.''
BBC ta tattauna da Farfesa Thumbi Ndung'u daga Jami'ar koyon aikin Likitanci ta Nelson Mandela da ke Durban wanda ya bayyana cewa ''Babu wata hujja da ke nuna cewa hakan gaskiya ne - kuma mun san cewa bakaken fata suna kamuwa da wannan cuta.''
3. Kofin shayi ba ya maganin coronavirus

Shan ruwa na da matukar amfani ga lafiya, amma shan shayi bai maganin coronavirus kamar yadda ake yadawa.
Kafafen yada labarai na kasar Kenya sun ruwaito cewa ana kiran mutane dama a waya ana ba su shawara kan cewa su shayi domin kare kansu daga coronavirus - kuma idan ba su yi hakan ba cutar za ta kashe su.
Chamfi ne da ake yadawa kuma babu tabbacin hakan a likitance.
Masana kimiyya a fadin duniya na gudanar da bincike kan riga-kafin coronavirus, sai dai ana ganin cewa ba za a samu wannan riga-kafin ba har sai tsakiyar shekara wannan shekara.
4. Babu amfanin aske gemu don kare kai daga coronavirus


Wani tsohon zanen hoto wanda ma'aikatar lafiya ta Amurka ta yi kan gemu da numfashi ya zama wani abu da aka yi amfani da shi wajen yada labaran karya inda ake cewa maza su aske gemunsu domin kare kansu daga coronavirus.
Kamfanin jaridar The Punch na Najeriya ta yi wani rubutu kan cewa ''Domin kare kai daga coronavirus, a aske gemu, gargadi daga CDC''
Cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Amurka ce ta fito da wannan zanen hoton inda take bayani kan irin gwamman salo na ajiye gemu a fuska da kuma irin gemun da bai kamata idan akwai shi a saka takunkumin rufe fuska ba.
Hoton na gaskiya ne kuma an yi shi ne tun a 2017 tun kafin barkewar coronavirus.
An yi irin wadannan labaran da jaridar The Punch ta wallafa a wasu kasashe kuma labaran sun yadu matuka.

Karin labaran da za ku so ku karanta

5. Malamin addini mai ikirarin yaki da coronavirus

Ikirarin da wani fasto ya yi cewa yana maganin coronavirus ba gaskiya ba ne.
An ta yada labarin David Kingleo Elijah a shafin Yotube na cocin Glorious Mount of Possibility inda yake cewa zai tafi China domin ''dakile coronavirus''.
A cikin bidiyon ya ce: "Zan je na dakile coronavirus ta hanyar amfani da mu'ujiza. Zan tafi China, Ina so na wargaza coronavirus."
Kwanaki kadan bayan haka, wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet sun yi zargin cewa faston ya tafi China amma an kwantar da shi a asibiti sakamakon kamuwa da coronavirus. Amma shafukan na intanet sun ambato shi da suna na daban - Elija Emeka Chibuke.
A zahiri, hoton da ya nuna shi a asibiti, hoto ne na Adeshina Adesanya, fitaccen dan wasan kwaikwayon Najeriya wanda aka fi sani da suna Pastor Ajidara, wanda ya mutu a asibiti a 2017.
6. Shan farfesu bai maganin coronavirus
A Najeriya, wani Fasto ya wallafa sakon bidiyo inda ya yi ikirarin cewa shan farfesu yana maganin coronavirus. An yi ta watsa wannan batu a manhajar WhatsApp.
Babu wani magani ko rigakafin coronavirus kuma ikirarin da faston ya yi bai yi cikakken bayani kan amfanin farfesu a fannin lafiya ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce barkewar cutar coronavirus ya haddasa watsuwar labaran karya sosai.
A Cape Verde, kasar da ke Yammacin Afirka, an watsa labarai a shafukan sada zumunta wadanda ke ikirarin cewa wani likita dan kasar Brazil ya bayar da shawara a rika shan wani nau'i na ganyen shayi mai suna fennel domin kauce wa kamuwa da coronavirus. Nan da nan farashin ganyen shayin ya tashi a kasuwanni, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP.
Ma'aikatar Lafiya ta Brazil ta gargadi mutane su guji watsa labarin da ke cewa ganyen shayin na fennel yana rigakafin coronavirus.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce wanke hannu a kai a kai na cikin manyan abubuwan da ke hana kamuwa da cutar ta coronavirus.

Karin labarai masu alaka













