Coronavirus: Rikicin Amurka da China na bayan fage

Cardboard cutouts of U.S. President Donald Trump and Chinese President Xi Jinping, with protective masks widely used as a preventive measure against coronavirus disease (COVID-19), near a gift shop in Moscow, Russia

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dangantaka ta sake tabarbarewa tsakanin Amurka da China sakamakon annobar coronavirus

Babu tantama, wannan wani lokaci ne mai wahala ga duniya kuma lokaci ne mai wahala ga dangantakar da ke tsakanin Amurka da China.

Shugaba Donald Trump ya sha kiran coronavirus ''Yar China'. Sakatarensa na harkokin waje Mike Pompeo ya kira cutar ''Yar Wuhan', abin da ke matukar bata wa China rai.

Shugaban da sakatarensa sun yi tir da China kan saken da ta yi daga farkon barkewar cutar.

Amma masu Magana da yawun China sun yi fatali da zargin cewa sun boye bayanai kan abin da ke faruwa a lokacin.

A shafukan sada zumunta a China, an yada labaran da ke cewa wani shirin rundunar sojin Amurka na kwayoyin cuta masu illa na kare dangi ne ya yi sanadiyyar annobar; wannan jita-jita ta samu karbuwa sosai.

Masana kimiyya sun nuna cewa kwayar cutar coronavirus, halitta ce daga Allah.

Amma wannan al'amarin ya fi karfin cacar baka, wani abu mai muhimmanci ne ke gudana.

A farkon wannan watan, lokacin da Amurka ta sanar da cewa za ta rufe iyakokinta ga matafiya daga kasashen Turai da yawa, ciki har da Italiya, gwamnatin China ta sanar da cewa za ta aika tawagogi da kayan aiki Italiyar, kasar da ta zama cibiyar annobar coronavirus.

Ta kuma aika agaji ga Iran da Serbia.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Wannan ya nuna cewa China ta zaku wannan annobar ta gushe, kuma ta bayyana kanta ga duniya a matsayin babbar mai fada a ji.

Tabbas, wannan wani salo ne na nuna karfin iko tsakaninta da Amurka- wacce a halin yanzu- take neman durkushewa.

Kuma aika 'yan tsirarun dakarun sojin samanta (Amurka) da ta yi a makare zuwa wani asibiti Italiya, ba zai zo daidai da kokarin da China ta yi ba.

Chinese medics posing for a group photo after landing on a China Eastern flight on March 13 at Rome"s Fiumicino international airport from Shanghai, bringing medical aid to help fight the new coronavirus in Italy

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, China ta aika ma'aikatan lafiya da kayan aiki ga kasashen da ke fama

Wannan wani lokaci ne da duka gwamnatocin kasashe ke fuskantar matsalolin da ba su taba fuskanta ba. Shugabanci zai yi wuya.

Za a tantance shugabannin siyasa bisa irin himmar da suka ba da wajen amfani da arzikin kasashensu don yaki da annobar.

Annobar ta barke a lokacin da dangantakar China da Amurka ke da nakasu. Yarjejeniyar kasuwancin da suka sanya wa hannu ta dan taimaka wajen daidaita rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.

Amma daga Chinar har Amurkar na kara zage damtse wajen shirya wa rikicin da ka iya barkewa nan gaba a yankin Asia-Pacific.

Kawo yanzu dai, China ta riga ta bude kwanjinta, ta kuma nuna cewa tana da karfin iko a fannin soji, musamman a yankinta.

Kuma a yanzu China ta kagu ta samu karbuwa a fadin duniya.

Annobar dai na barazanar jefa dangantakar Amurka da China cikin mawuyacin halin da ya fi na da. Wannan na da muhimmanci ga inda aka dosa a yayin wannan annoba da kuma bayanta.

Idan aka shawo kan coronavirus, sabon wankan da tattalin arzikin China zai yi, zai taka muhimmiyar rawa wajen habako da tattalin arzikin duniya da ya durkushe.

Amma a yanzu dai, agajin da China za ta bayar na da muhimmanci wajen yaki da coronavirus.

Dole a ci gaba da rarraba bayanan kiwon lafiya.

Haka kuma, China na samar da kayan aikin asibiti kamar takunkumin rufe fuska da rigunan kare jiki, wadanda kuma ke da muhimmanci wajen kula da masu dauke da coronavirus, kuma ana bukatar wadannan kayayyakin da yawa.

Babu shakka, China ce cibiyar masana'antu ta duniya musamman masana'antun kayan kiwon lafiya, kuma za ta iya fadada ayyukanta fiye da sauran kasashe.

China na amfani da wannan dama, amma kamar yadda masu sukar Shugaba Trump da dama suka ce, shi ne ya tafka babban kukure.

Daga farko, gwamnatin Trump ta ki amincewa da girman matsalar, ta kuma ga cewar wannan dama ce ta nuna "Amurka ce farko" a ko da yaushe.

Amma abin da yake muhimmi yanzu shi ne shugabancin duniya.

Bayanan bidiyo, Ta yaya mutum zai san yana da coronavirus?

Wasu kwararru kan nahiyar Asiya, Kurt M Campbell- wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin sakataren cikin gida na gabashin Asiya a lokacin mulkin Obama- da Rush Doshi, suka ce a wata makala da ta fito kwanan nan:

"Kallon da ake yi wa Amurka a matsayin shugabar duniya a shekaru 70 da suka gabata, bai tsaya kan arzikinta da karfin ikonta ba, sai kan bin ka'idar shugabancin cikin gida da samar da ababen more rayuwa ga duniya da kuma iyawarta wajen tabuka wani abu a lokacin wata annoba a fadin duniya."

Annobar coronavirus, a cewarsu, "na gwada duka bangarori uku na shugabancin Amurka. Kawo yanzu, Amurka ta fadi warwas.

Yayin da take tangal-tangal, China na kara kaimi wajen amfani da damar da Amurkar ke bata ta hanyar tafka kura-kurai, tana maye gurbin Amurkar a matsayin shugabar duniya a lokacin annoba."

Wasu na iya yin tantama kan wannan matsaya, wasu na cewa ya za a yi China ta nemi suna a wannan lokaci- ganin cewa wannan annobar a Chinar ta fara bulla.

A lokacin da cutar ta fara bayyana, China ta boye wa sauran duniya. Amma tun daga wannan lokaci, ta yi amfani da arzikinta mai dumbin yawa yadda ya kamata.

Kamar yadda Suzanne Nossel, shugabar kungiyar masu fafutukar kare hakkin 'yan jarida ta PEN ta rubuta a wata Makala a shafin intanet na mujallar Foreign Policy: "Abin tsoro ne yadda daga farko aka boye kuma aka ki tafi da annobar nan yadda ya kamata, wanda ka iya janyo tashin hankali.

''Amma yanzu China ta kaddamar da gagarumin kamfe na farfaganda a duniya don ta mantar da duniya yadda ta yi daga farkon annobar, sannan ta rage kaifin ciwon da ta haifar saboda rawar da ta taka wajen bazuwar cutar a duniya, kuma ta nuna inda kokarinta ya sha bamban da na sauran kasashen duniya masu fada a ji musamman ma Amurka."

Masu sharhi da daman a kasashen yamma na ganin China za ta zama mai karfin iko kuma mai kishin kai, amma suna fargabar cewa wannan salon zai kara zuzuta tasirin annobar da durkushewar tattalin arzikin da zai biyo baya.

Amma tasirin da wannan zai yi ga matsayin Amurka a duniya, na iya fin komai muni.

Chinese President Xi Jinping wearing a mask as he GESTURES to a coronavirus patient and medical staff via a video link at the Huoshenshan hospital in Wuhan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Xi Jingping ya kagu China ta maye gurbin Amurka wajen karfin iko a duniya

Kawayen Amurka na sa ido

Kawayen Amurka na nan suna kula da duk abin da ke faruwa.

Ba lallai su soki gwamnatin Trump ba a bayyane, amma da yawa daga cikinsu na sane da bambancin gwamnatin da China; da rikicin kimiyya tsakanin Amurkar da China (na kamfanin Huawei) da rikicinta da Iran da sauran batutuwa.

China na amfani da ayyukanta a lokacin wannan annoba wajen samun wurin zama don wata manufa ta daban nan gaba - babu mamaki, so take ta yi gaggawar zama 'mai karfin fada a ji a duniya.

Yakin da take yi da coronavirus a makwabtanta Japan da Korea Ta Kudu- da kuma samar da kayan aikin asibiti masu muhimmanci ga Tarayyar Turai, na iya nuni ga wannan fatan nata.

Campbell da Doshi, a makalarsu, sun hada wannan lamari da yadda Burtaniya ta rasa karfin ikonta karara.

Sun ce yunkurin Burtaniya na kwace hanyar ruwa ta Suez (Suez Canal) a 1956 da aka tarwatsa "ya nuna karara lalacewar karfin ikon Burtaniya, kuma ya kawo karshen wa'adinta a matsayin mai karfin fada a ji a duniya".

"Yanzu, wadanda ke rike da madafun iko a Amurka sai su gane cewa idan Amurkar ba ta zage dantse ba a yanzu, annobar coronavirus na iya mayar da Amurka kamar Burtaniya."