Coronavirus: Hotunan yadda annoba ta sauya duniya da aka dauka da tauraron dan adam

Car rentals at Phoenix

Asalin hoton, Maxar

Hotunan da aka dauka da tauraron dan adam sun nuna yadda wasu wurare da aka sani da taruwar jama'a suka zama tamkar kufai sakamakon annobar coronavirus.

A birnin Vermont na Amurka babu kowa a wajen ajiye motoci saboda masu wasan zamiyar kankara sun kauracewa wajen shakatawa da ke Killington. An haramta taruwar mutane da suka wuce 50 a jihar, an rufe mashayu an kuma hana kantunan sayar da abinci aike wa da abinci wasu wuraren har sai 6 ga watan Afrilu.

Wajen hayar motoci na birnin Phoenix babu kowa, idan aka kwatanta da hotunan da kamfanin Fasaha na Maxar ya dauka inda a baya ke cike taf da mutane a farkon watan nan.

Babu jirage sosai a filin jirgin sama na birnin Salt Lake.

Wannan hoton na kasa ya nuna yadda cunkoson motoci ya yi yawa a tsakiyar birnin Moscow na Rasha, inda jami'ai suka rufe dukkan makarantu da hana taruwar jama'a da suka wuce 50.

Traffic jam in Moscow, Russia

Asalin hoton, Maxar

A Iran kuwa inda aka samu dubban mutane masu dauke da coronavirus, an rufe wajen ibada na Imam Reza a Mashhad, saboda hadarin yaduwar cutar.

Hotunan tauraron dan adam daga kamfanin Kimiyya na Maxar