Coronavirus: Shin annoba ba ta shiga garuruwan Makkah da Madina?

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da annobar coronavirus ta fara kutsawa wasu kasashen duniya a farkon watan Fabrairu bayan bullarta a China a Disambar 2019, wasu Musulmai ke cewa annobar ba za ta shiga garuruwa masu tsarki na Makkah da Madina ba.
Sai dai samun mutum na farko mai dauke da cutar a kasar Saudiyya ranar 2 ga watan Maris din 2020, ya sa mutane da yawa sun fara samun fargaba, da fatan ta tsaya a sauran garuruwan kasar ban da Makkah da Madinah.
Fatan nasu bai gushe ba saboda mafi yawa sun dogara da cewa akwai hadisan da aka ruwaito Annabi SAW ya ce 'babu annobar da za ta shiga garuruwan masu aminci'.
Mutane da dama sun yi ta ganin laifin Saudiyya kan yadda ta tsagaita yin dawafi tare da bayar da dama mutane kadan suna shiga tawaga-tawaga don gudun kar a sami cakuduwa tsakanin mutane da gudun kara watsuwar annobar coronavirus tsakanin masu dawafi.
Masu korafin suna cewa ai Annabi SAW ya ce: ''Annoba da Dujal ba sa shiga garin Madina, saboda haka suna cewa abin da ya kamata shi ne a bar mutane su ci gaba da yin dawafinsu kamar yadda suka saba ko yaushe, ko da kuwa duniya na fama da annobar coronavirus mai saurin yaduwa.''


Sai dai duk da matakan da Saudiyyar ta dauka na hana shiga biranen masu tsarki a wani matakin hana yaduwar cutar coronavirus mai shafar numfashi, sai ga shi daga baya an samu wadanda cutar ta kama a garin Makkah.
Sannan a ranar Talata 24 ga watan Maris cutar ta kashe mutum na farko a kasar a garin Madina.
Wannan dalili ya sa muka tuntubi Malam Ibrahim Disina, wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, wanda kuma ya yi karatu a Madina, shin ko gaskiya wannan magana tana da tushe a Musulunci?
Malamin ya ce: ''Gaskiya ne a wani Hadisi da Bukhari da Muslim suka ruwaito ya fadi wata magana kamar haka, amma kuskuren fahimta ya sa wasu ke zaton abin da Hadisin yake nufi kenan.
''Malamai masu fashin baki da sharhin Hadisai irin su Ibnu Hajr cikin shahararren littafinsa Fathul Bari, sun bayyana cewa lafazin "Adda'un" (anoba) da Annabi SAW ya ambata a Hadisin yana nufin; wani nau'in rashin lafiya ne da ya yi kama da karzuwa mai haifar da manyan kuraje a fatar mutum watau a duk jikin mutum, shi ne Annabi ke nufin Allah ya yi alkawarin bai wa garin Madina kariya da watsuwarsa a matsayin Annoba.

Asalin hoton, Getty Images
Malam Disina ya kara da cewa: ''Amma annobar da kan faru lokaci-lokaci kam tana shiga garin Makka da Madina, domin ko a zamanin Annabi an yi Annobar da aka yi ta mutuwa kamar yadda Bukhari ya ruwaito.
''Sannan ko a cikin tarihin garin Makkah da Madinan a kan sami barkewar annoba kamar yadda aka samu masu coronavirus a yanzu," in ji Disina.
''Ko cikin shekara ta 1228 bayan Hijira dai-dai da shekara ta 1814 Miladiyya, an sami gagarumar annobar da dubban maniyyata suka mutu wanda hakan ya jawo a wannan shekarar ba a yi aikin Hajji ba'', a cewar malamin.










