An sace matan Fulani akalla 20 a Borno

Asalin hoton,
Rahotanni daga Nigeria sun ce wasu 'yan bindiga sun sace matan Fulani akalla 20 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Sai dai wani jagoran al'ummar fulani ya shaida wa BBC cewar wasu 'yan bindiga sun sace matan Fulani 40 a wata ruga da ke kusa da garin Chibok na jihar Borno a Nigeria.
Shugaban wanda baya son a bayyana sunansa, ya ce 'yan Boko Haram ne suka sa ce matan a ranar Asabar.
Chibok ne garin da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai fiye 200 makonni bakwai da suka wuce, kuma kawo yanzu ba a ceto 'yan matan ba.
Gwamnatin Jihar Borno da jami'an tsaron Nigeria sun ce ba su da labari game da batun.
Sai dai wani dan kungiyar sintiri a Borno, Alhaji Tar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewar mata 20 aka sace a rugar Fulanin.
A cewarsa, 'yan bindigar sun je rugar Fulanin da rana ne a lokacin maza sun tafi kiwon shanu kafin su sace 'yan matan da karfin bindiga.
Alhaji Tar din kuma ya kara da cewar 'yan bindigar sun tafi da maza uku wadanda suka nemi hana sace matan Fulanin.










