An kashe jami'an tsaro 24 a Buni Yadi

Rahotanni daga garin Buni Yadi na Jihar Yobe sun ce an kashe jami'an tsaro kusan 24 a wani hari da 'yan Boko Haram suka kai a sansanin jami'an soji a jihar.
Mazauna garin sun ce 'yan Boko Haram din sun je garin cikin arayin motoci goma da mota mai suka daya.
A cewar 'yan garin, 'yan Boko Haram din sun ce sun zo daukar fansa a kan sojoji ne a don haka ba za su taba fararen hula ba.
'Yan Boko Haram din kuma sun kona gine-gine ciki hadda gidan Hakimin garin da motocinsa.
Wata majiyar tsaro a Nigeria ta shaidawa BBC cewar an kashe sojoji 11 da 'yan sanda 13 a harin da ya aka kai a yammacin ranar Litinin.
Jihar Yobe na daga cikin jihohi uku da ke karkashin dokar ta baci, kuma 'yan Boko Haram na yawan kai hare-hare a Jihar.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Boko Haram ke ci gaba da rike 'yan matan Chibok da suka sace fiye da makonni shida da suka wuce.






