Mutane 30 sun mutu a hadarin mota a Yobe

Rahotanni daga Jihar Yobe dake Arewacin Nigeria sun ce kusan mutane 30 ne suka kone kurmus a sakamakon wani mummunan hadarin mota.
Hadarin, wanda ya faru a safiyar ranar Litinin, ya ritsa da motoci uku ne, kuma ya faru ne a kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum.
Wasu rahotannin sun ambato Hukumar kiyaye hadarruka ta jihar Yoben, tana cewa mutane 55 ne suka hallaka a hadarin.
A ranar Lahadi ma mutane sama da 10 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin mota tsakanin garin Alkali zuwa garin Gashua a jihar ta Yobe.






