An kashe mutane 42 a Gurmushi na Borno

Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga garin Gurmushi da ke karamar hukumar Marte ta jihar Borno sun ce an kashe mutane akalla 42 a wani hari da 'yan bindiga suka kaddamar a ranar Laraba da safe.
'Yan bindigar -- wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne -- sun kuma raunata wasu mutane tare da kona daukacin gidajen garin.
Wata mata da ta tsira daga harin ta shaidawa BBC a harshen Kanuri cewa "Ina daga cikin wadanda suka tsira, an kona garin baki daya. Na ga gawarwaki 42".
A halin yanzu dai an garzaya da wasu daga cikin mutanen da suka samu raunuka zuwa wani gari da ke kan iyakar Nigeria da kasar Kamaru.
Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a kan kauyukan da ke jihar Borno da Yobe.
A halin da ake a yanzu dai fiye da makonni shida kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 a wata makaranta da ke Chibok a jihar Borno.






