Sojoji sun farma 'yan Boko Haram a Bauchi

Asalin hoton, Nigeria Army
Rahotanni daga Jihar Bauchi da ke Nigeria sun ce jiragen yaki na soji sun yi luguden wuta a sansanonin da ake zargi na 'yan Boko Haram ne a wasu dazukan jihar.
Mazauna kananan hukumomin Ganjuwa da Darazo sun ce sun hango jiragen yaki na soji sun doshi dazukan jihar, kuma daga bisani sun ji karar fashewar bama-bamai.
Wannan lamarin ya faru ne a cikin daren ranar Alhamis.
Ana zargin cewar 'yan Boko Haram na gudanar da ayyukansu a wasu kananan hukumomi na jihar Bauchi da kuma karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa.
Kungiyar Boko Haram mai cibiya a yankin arewa maso gabashin Nigeria ta kashe dubban mutane tare da raunaka wasu da dama.







