Boko Haram: Malamai 170 sun mutu a Borno

Asalin hoton, Reuters
Kimanin malaman makaranta fiye da 170 ne suka rasa rayukansu, a hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a jihar Borno da ke Nigeria.
Reshen kungiyar ta jihar Borno ce ta shaida wa BBC hakan a Abuja.
Lamarin da ya jefa malaman makaranta cikin tsoro, yayin da wasu ma ke tunanin barin aikin malanta.
Kungiyar ta ce alkaluman jimilla ne na malaman da suka mutu a jihar, tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hari a shekarar 2009 zuwa yanzu.







