Sojoji sun harbi motar shugabansu a Maiduguri

Asalin hoton, AP
Rahotanni daga Maiduguri a jihar Borno na cewa wasu sojoji da suka fusata sun harbi motar shugaban rundunar sojoji na birnin, Manjo Janar Muhammad.
Lamarin ya auku ne a ranar Laraba da safe, inda rahotannin suka bayyana cewa, sojojin sun fusata ne sakamakon abin da suka kira rashin kulawa da bukatunsu daga shugabanninsu.
A cewar rahotannin sojojin sun kuma zargi shugabanninsu da yi musu turin jeka ka mutu a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.
Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Najeriya ke bukatar a sabunta dokar ta baci a jahar ta Borno da Yobe da kuma Adamawa.






