An kone gidaje 300 a Borno

Asalin hoton, AFP
Rahotanni na cewa an kai wani hari a kauyen Limankara a karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Wadanda suka kai harin sun kone gidaje da dama da kuma shaguna.
Maharan wadanda ake zargin 'Yan boko haram ne sun tarwatsa gadar da ta hada garin Limankara a Gwoza da kuma Michika dake Jihar Adamawa.
Sai dai babu asarar rayuka saboda mazuna kauyen sun tsere bayan sun samu labarin wadanda ake zargin na kan hanyar farma kauyen.







