Soji sun kashe 'yan Boko Haram 38 a Damboa

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kashe mayakan jama'atu ahlis sunnah lidda'awati wal jihad, da ake kira Boko Haram 38 a fafatawar da suka yi daren Alhamis, a Damboa dake jihar Borno.
Kakakin rundunar a Maiduguri, kanar Muhammad Dole ya ce soja daya ya mutu a arangamar yayin da wasu biyu su ka jikkata.
Rundunar ta ce ta kwace manyan bindigogi da motoci shake da abubuwa masu fashewa daga wurin mayakan.
Ta kuma ce jiragen yaki na soji na ci gaba da bibiyar maharan.
Kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan arangamar.






