An sace ma'aikatan Red Cross a Syria

Kungiyar agaji ta duniya Red Cross ta ce an sace ma'aikatanta su bakwai a arewa maso yammacin Syria.
Wata mai magana da yawun kungiyar a Damascus Rima Kamal ta shaidawa BBC cewa ma'aikatan kungiyar su shidda da kuma wani ma'aiakacin sa kai a kungiyar agaji ta Red Crescent na Syria an ritsa su da bakin bindiga aka kuma yi awon gaba da su a kusa da garin Saraqeb a gundumar Idlib.
Ta ce tawagar ma'aikatan suna kan hanyar su ce ta komawa Damascus a yau a motarsu da aka zana tambarin Red Cross balobalo a jikinta.






