Za a rabawa 'yan gudun hijrar Syria katuna

Shirin ba da taimakon abinci na majalisar dinkin duniya ya ce, zai rabawa 'yan gudun Hijrar Syria wa su katuna domin tabbatar da cewa sun sami taimakon abincin da su ke bukata.
Kowanne kati na mutum guda na dauke da kusan dala ashirin da bakwai a wata guda, wanda kuma za ayi amfani da su wajen sayen kayayyaki da ga jerin abubuwan da ke cikin daruruwan kantunan da ke kusa da iyakar Syria wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.
Hakan dai na nuni da cewa, 'yan gudun Hijrar ka iya sayen wasu nau'ikan kayan abinci kamar madara da chese wanda ba kasafai aka fiya gani ba a cikin irin abincin da ake ci.
Wannan shiri na son ganin an baiwa mutane dubu dari takwas irin wannan kati zuwa karshen shekara.







