Ana yawan hadarin jirgin ruwa a Najeriya

A Najeriya, ana fama da matsalar hadarin jiragen ruwa da ke haddasa asarar rayuka a wasu bangarorin kasar.
Kusan mutum Sittin ne suka mutu cikin makwanni biyu a wasu hadura biyu da suka auku a jihar Niger da ke arewacin kasar.
Masana harkokin sufurin ruwa na ganin cewa idan matuka jiragen ruwan za su kasance masu bin ka'ida da za a kauce wa aukuwar irin wadannan hadura.






