Maniyyata Hajji sun tsallake rijiya da baya

Wani jirgin sama dauke da maniyyata aikin hajji 'yan jirgin yawo, su kimanin dari hudu, ya yi saukar gaggawa a Sakkwato bayan tayoyinsa sun fashe.
Rahotanin da muka samu sun ce Jirgin na kamfanin Kabo ya tashi ne daga Kano.
Kuma an sauki maniyyatan a wani babban Otal da ke birnin Sakkwato.







