Za'a sake shari'ar Husni Mubarak

Wata kotu a Masar ta soke hukuncin daurin rai-da-rai da aka yiwa tsohon shugaban kasar Husni Mubarak.
Kotun ta yi umarnin a sake sauraron shari'ar da aka yi masa bisa tuhumar gaza kare rayukan daruruwan masu zanga-zangar da suka tilasta masa barin kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce.
Alkalin kotun ya ce za'a sake wa Mr Mubarak sabuwar shari'a ce tare da 'ya'yansa Alaa da Gamal da kuma tsohon ministan cikin gida Habib al-Adly.
Daruruwan Magoya bayan tsohon shugaban kasar da suka hallara a kotu sun baiyana farin cikinsu da hukuncin.
Daya daga cikinsu yace "wannan hukunci yayi daidai kuma in Allah ya yarda za'a gano cewa Mubarak da dukkan mataimakansa ba su yi laifin komai ba."
Sai dai kuma wakilin BBC yace mafi yawan al'ummar Masar sun yi takaicin hukuncin da aka yiwa Mr Mubarak a baya, bisa laifin kasa tsare rayukan masu zanga-zanga maimakon baiwa jami'an tsaro umarnin kisan talakawa.







