An kashe ma'aikatan Polio a Pakistan

'Yan bindiga sun harbe wasu mata dake aikin alluran riga kafin cutar shan Inna -- ta Polio a Pakistan.
Hare haren sun faru ne a wasu yankuna 3 daban daban na birnin Karachi mafi girma a ƙasar da kuma a Peshawar.
Jami'an yankin sunce a halin yanzu an dakatar da aikin riga kafin a waɗannan yankuna.
Ba a dai san kowa ya harbe matan ba, to amma a baya shugabannin ƙungiyar Taliban sunce ana amfani da aikin ne domin leƙen asiri, sannan kuma wani ƙoƙari ne na hanawa musulmi haihuwa.
Cutar ta Polio dai ta yi katutu a Pakistan , kuma a makon nan hukumar lafiya ta duniya ta ƙaddamar da wani aiki a dukkanin faɗin ƙasar domin baiwa yara magungunan riga kafin kamuwa da cutar.







