Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Lewandowski, Neymar, Ronaldo, Carrasco, Pogba, Rabiot, Antony

Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta kammala cinikin dan wasan Bayern Munich da Poland kuma mai kai hari Robert Lewandowski, dan shekara 33, kan fam miliyan 34. (Telegraph - subscription required)

Kaftin din Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, yana nuna damuwa kan musayar 'yan wasa karkashin jagorancin sabon manajan kulob din Manchester United Erik ten Hag tare da tunanin barin Old Trafford. (Record - in Portuguese)

Tsohon eja din Neymar ya ce dan wasan gaba na Brazil mai shekara 30 yana mafarkin wata rana ya zama zakaran gasar Champions League a Paris St-Germain ''ba kuma zai gajiya ba har sai mafarkinsa ya zama gaske." (Goal - in Spanish)

Dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 30, na duba yiwuwar komawa Manchester United ko ci gaba da kasancewa a Brentford. (Sky Sports)

Dan wasan tsakiya na Manchester United da France Paul Pogba, mai shekara 29, yana da yarjejeniyar komawa Juventus ba tare da ko sisi ba. (Sky Italia - in Italian)

Chelsea za ta kara da Manchester United da Ajax da Brazil kan dan wasa winger Antony, bayan tattaunawa da wakilan dan wasan mai shekara 22. (Football365)

Manchester United, Chelsea da Tottenham na duba yiwuwar sanya hannu kan kwantiragin dauko dan wasan Atletico Madrid da Belgium winger Yannick Carrasco, mai shekara 28, a wannan kakar kan farashi fam miliyan. (AS - in Spanish)

Dan wasan tsakiya na Faransa, Adrien Rabiot na son barin Juventus domin komawa kulub din Premier League. Mai shekara 27, wanda shekara daya ta rage ma sa a kwantiraginsa, zai kasance a kasuwa kan fam miliyan 15 zuwa 20. (Telegraph - subscription required)

Chelsea na son dauko dan wasan Juventus da Netherlands Matthijs de Ligt mai shekara 22. (Sky Italia)

Leicester City ka iya maida dan wasan tsakiya na Faransa, Benjamin Bourigeaud, mai shekara 28, watakil kan farashin fam miliyan 8. (Jeunes Footeux - in French)

AC Milan na duba yiwuwar rattaba hannu kan kwantiragin dauko dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, mai shekara 24, ta hannun ejan shi dan Brazil wanda ya yi balaguro zuwa kulub din na Italiya domin tattaunawa. (TuttoMercatoWeb - in Italian)