Nkunku ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da wasa a RB Leipzig

Asalin hoton, Reuters
Christopher Nkunku ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda kaka biyu a RB Leipzig.
Kenan dan wasan tawagar Faransa zai ci gaba da taka leda a kungiyar da ke buga Bundesliga har zuwa karshen kakar 2026.
An yi ta alakanta dan wasan mai shekara 24 da cewar zai koma buga tamaula a bana a Chelsea ko Manchester United, yanzu zai ci gaba da zama a Jamus.
An zabi Nkunku a matakin fitatcen dan wasa a Bundesliga a kakar da aka kammala ta 2021-22, ya kuma dauki German Cup a cikin watan Mayu.
Nkunku ya ci kwallo 20 ya kuma bayar da 14 aka zura a raga a karawa 34 a Lik, wanda ya taimaka RB Leipzig ta yi ta hudu a teburin Bundesliga da aka karkare.







