Kasuwar 'yan kwallon kafa : Makomar Antony, Bergwijn, Ward-Prowse, Lewandowski, da Cucurella

Dan wasan gaba na Ajax dan Brazil Antony, mai shekara 22, ya kuduri aniyar tafiya Manchester United a bazaran nan. (Goal)
Kociyan Barcelona Xavi na rokon Ousmane Dembele, ya yarda ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar, yayin da Chelsea ke nuna saha'awarta a kan dan wasan na Faransa. (Goal)
Mai yuwuwa a sayar da dan wasan baya na Manchester United da Ingila Brandon Williams, mai shekara 21, a kan fam miliyan 10. (Sun)
Ajax za ta kara taya dan wasan gaba na gefe na Tottenham Hotspur dan Holland Steven Bergwijn, mai shekara 24, amma kuma kungiyar ta Premier ba za ta karbi kudin da yake kasa da fam miliyan 25 ba. (Sky Sports)
Southampton na kokarin hana kungiyoyin Manchester City da Manchester United da Tottenham da West Ham zawarcin dan wasanta na tsakiya, dan Ingila James Ward-Prowse mai shekara 27, inda ta yi masa farashin fam miliyan 75. (Give Me Sport)
Babban jami'in Bayern Munich Oliver Kahn ya ce yana sa ran Robert Lewandowski, ya ci gaba da zama a tare da zakarun na Jamus a bazaran nan. (Sky Sports)

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi nisa a tattaunawar da take yi ta cinikin dan bayan Brighton da Sifaniya Marc Cucurella. (Football Insider)
Leeds United na duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na gefe na PSV Eindhoven da Holland Cody Gakpo, a bazaran nan a matsayin wanda zai maye gurbin Raphinha,na Brazil, wanda Arsenal ke so. (Foot Mercato)
Leeds ta yi wa Raphinha kudi a kan fam miliyan 65, inda Tottenham, da Chelsea da Barcelona ke sha'awarsa. (Fabrizio Romano)
Nice na neman kulla yarjejeniyar daukar aron mai tsaron ragar Chelsea, dan Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 27. (Foot Mercato)
Chelsea za ta bayar da damar sayar wa West Ham dan wasanta mai kai hari, dan Albania Armando Broja, mai shekara 20, inda ake sa ran za ta taya shi fam miliyan 25. (Express)

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Brighton ta sayo dan wasan tsakiya na Reims da Zimbabwe Marshall Munetsi, mai shekara 26 domin maye gurbin Yves Bissouma, dan wasan tsakiyarta na Mali wanda ya tafi Tottenham. (Mail)
Bisa ga dukkan alamu golan Liverpool dan Jamus Loris Karius, mai shekara 29, na shirin jarraba sa'arsa a wata kungiyar, kasancewar ba makawa zai bar Anfield. (Sky Germany)
Shi kuwa dan wasan gaba na Real Madrid da Sifaniya Marco Asensio, mai shekara 26, ya fi kaunar tafiya Liverpool ne maimakon AC Milan. (Mail)
Chelsea na jiran tafiyar Romelu Lukaku, aro Inter Milan ta kammala kafin, kungiyar ta tunkari maganar sayen dan gaban Manchester City da Ingila Raheem Sterling. (Sky Sports)
Matashin dan wasan Brazil Vinicius Jr, mai shekara 21, ya ce, zai ci gaba da zama a Real Madrid duk da sha'awarsa da Paris Saint-Germain ke yi. (Mail)











