Harin cocin Owo: Yadda aka yi jana'izar Kiristocin da 'yan bindiga suka kashe

Mutanen da aka kashe a harin coci na Jihar Ondo
Bayanan hoto, A yau Juma'a, 17 ga watan Yuni aka yi jana'iza tare da yi wa Kiristocin da 'yan bindiga suka kashe a harin coci na Jihar Ondo binnewar bai-ɗaya
Mutanen da aka kashe a harin coci na Jihar Ondo
Bayanan hoto, Mutum 40 aka binne a yau ɗin bayan gudanar da addu'o'i, inda Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu da matarsa suka halarata
Mutanen da aka kashe a harin coci na Jihar Ondo
Bayanan hoto, Tun bayan kisan masu ibadar da ke tsaka da addu'o'i ranar 5 ga watan Yuni, garin Owo ya shiga cikin alhini
Mutanen da aka kashe a harin coci na Jihar Ondo
Bayanan hoto, Rahotanni na cewa hukumomi sun yanke shawarar mayar da wurin da aka binne su ya zama wurin tunawa da waɗanda harin ya shafa
Mutanen da aka kashe a harin coci na Jihar Ondo
Bayanan hoto, Gwamnatin Najeriya ta ce mayaƙan ƙungiyar ISWA ne masu iƙirarin jihadi suka kai hari kan cocin da ke kusa da fadar basaraken yankin
Mutanen da aka kashe a harin coci na Jihar Ondo
Bayanan hoto, Zauwa yanzu jami'an tsaro a Najeriya ba su kama kowa ba da ake zargi da kai harin, saɓanin wasu rahotanni da aka yaɗa a shafukan zumunta
Mutanen da aka kashe a harin Owo

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Gwamnonin yankin kudu maso yammacin ƙasar, inda ƙabilar Yarabawa suka fi rinjaye, sun ayyana kwana huɗu don yin makokin mutanen

Hotuna da sunayen marigayan

Gwamnatin Jihar Ondo ta wallafa sunayen mutanen da aka yi wa jana'iza sakamakon harin, waɗanda kuma BBC ta gani.

Mutanen da aka kashe a harin Owo
Ondo
Jihar Ondo

Asalin hoton, BBC

Jihar Ondo
Jihar Ondo