Sunaye da fuskokin mutanen da suka mutu a harin cocin Owo

Mutanen da suka mutu a harin cocin Owo

Asalin hoton, Empics

A ranar Lahadi 5 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka dira cocin St. Francis Xavier da ke garin Owo a jihar Ondo dake Kudu maso Yammacin Najeriya.

Ba su bata lokaci ba suka buda wuta kan masu ibada inda suka kashe mutum 40 tare d jikkata wassu da dama da yanzu haka ke jinya a asibiti.

Binciken ƴan sanda ya nuna cewa maharan sun yi shiga ne tamkar wadanda suka zo ibada, kafin su shiga harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Harin ya yi matukar tsorata al'umma musamman mazauna yankin Kudanci, da ba kasafai ake ganin irin wadannan hare hare ba.

Ga wasu daga cikin fuskokin da suka mutu da kuma labarinsu

Caroline Agboola

Caroline Agboola

Asalin hoton, Caroline Agboola

Caroline Agboola dattijuwa ce da aka harbe har lahira a harin.

'Yarta ta fada wa BBC cewa mahaifiyarta ta na sana'ar sayar da kosai ne kafin ta hadu da ajalinta.

Mai gidanta ya mutu shekarun baya

Veginus Nwani

Veginus Nwani

Asalin hoton, Veginus Nwani

Mr Veginus Ani ya mutu a harin ne tare da 'yarsa Chidiogo.

Babban ɗansa na tare dasu amma bai yi ko kwarzane ba.

Rahotanni sun ce bayan wucewar maharan dan ya dauki kanwarsa a kafada har asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Chidiogo Nwani

Chidiogo Nwani

Asalin hoton, Chidiogo Nwani

Chidiogo Nwani ta mutu tare da mahaifinta wato Veginus Nwani. Shekarunta na haihuwa goma sha daya.

Umunna

Umunna

Asalin hoton, Umunna

Umunna da dansa sun mutu a tare a harin na ranar Lahadi.

Bayan harin an same shi rungume da dan shi alamun cewa ya yi kokarin bashi kariya ne.

Labarin da ke yawo shine maharan sun lura yana kokarin ba dan nasa kariya saboda haka sai suka harbe su duka biyu.

Umunna na da shagon sayar da kayan wuta ne a garin na Owo.

Ozurumba Bridget

Ozurumba Bridget

Asalin hoton, Ozurumba Bridget

Itama Mama Ozurumba Bridget na daga cikin wadanda suka rasa ransu a harin.

Kuma yanzu haka danta wanda shima bala'in ya rutsa dashi yana jinya a asibiti.

Madam Onuoha

Madam Onuoha

Asalin hoton, Madam Onuoha

Papa Onuoha

Papa Onuoha

Asalin hoton, Papa Onuoha

Mama Onuoha da Maigidanta da ake kira da Papa Onuoha mata da miji ne da suka mutu a wannan hari.

Sai dai dansu da suke tare da shi bai ji ko da rauni ba.

Papa Onuoha na aikin yankar fulawa ne yayin da matarsa ke tsaron tireda.

Gwamnatin Najeriya ta ce ISWAP ce ta kai harin

Hukumomin Najeriya sun ce suna zargin kungiyar Boko Haram reshen ISWAP da ke Afrika ta Yamma ce ta kai harin na cocin St Francis Catholic da ke Owo a jihar Ondo ranar Lahadi.

Adadin wadanda aka kashe a harin ya kai mutum 40, kuma da dama sun jikkata.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya tabbatar wa da yan jarida haka, bayan kammala wani taron majalisar tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Idan har ta tabbata cewa ISWAP ce ta kai harin, to zai zama na farko da kungiyar ta taba kaiwa a Kudancin Najeriya.

Sai dai har yanzu kungiyar ba ta fito da bakinta ta dauki alhakin harin ba.