Harin Owo: Hotunan halin da ake ciki bayan kai hari coci a Ondo

Har yanzu ƴan Najeriya na cikin kaduwa bayan mummunan harin da aka kai kan masu ibada a wani coci a jihar Ondo.

A ranar Lahadi ne aka kai hari inda mutane da dama suka rasa rayukansu, ciki har da ƙananan yara.

Dangin waɗanda suka mutu suna cikin kaɗuwa har yanzu.

victims
coci

Harin ya sanya tsoro da firgicci a zuƙatan mutane da dama da suka haɗa da kiristoci da shugabannin majami'u.

An yaɗa hotuna masu ɗaga hankali a shafukan sada zumunta na wadanda suka jikkata a harin.

An kai wasu da dama asibiti inda suke karɓar magani.

coci
coci
coci
coci

Najeriya na fuskantar munanan hare-haren ƴan bindiga a sassan ƙasar.

Mutane a faɗin ƙasar na nuna damuwa kan gazawar gwamnati wajen magance ƙaruwar rashin tsaro da ake fama da shi.

Hukumomi sun sha alwashin gano waɗanda suka kai harin.

coci

Zuwa yanzu harabar cocin ta kasance a killace, sai dai manyan mutane musamman ƴan siyasa sun kai ziyarar jaje.

victims