Fabindia: Yadda kamfanin tufafi a Indiya ya gamu da fushin masu ra'ayin-rikau

Sanannen kamfanin sayar da tufafin nan na kasar Indiya, Fabindia, wanda ya yi fice wajen sayar da tufafin kabilu, ya samu kansa cikin takun-saka da masu ra'ayin rikau na kasar. Me ya sa kamfanin ya samu kansa cikin mummunan tarkon 'yan kishin kasa?
A watan Oktoban da ya gabata wani mai shirya fina-finan Bollywood ya fitar da wata wasika mai kalubalantar kamfanin sarrafa tufafin mafi girma a kasar.
Vivek Agnihotri shi ne wanda ya shirya fim din The Kashmir kuma sananne ne wajen goyon bayan Jam'iyar Bharatiya Janata (BJP) mai mulkin kasar.
Bacin ransa kai-tsaye a kan Fabindia ne, kamfanin kayayyakin sakar hannu mafi girma a kasar Indiya.
A cikin watan ne kamfanin ya janye wani talla game da lokacin bukukuwa bayan kalubalantarsa da kungiyoyin masu ra'ayin rikau suka yi masa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
A wasu martani biyar a jere a shafin Tuwita, Mista Agnihotri ya zargi Fabindia da kasancewa dan gaban-goshin kungiyoyin masu sassaucin ra'ayi na kasar Indiya ''marasa bin al'ada'' da ke da alaka da babbar jam'iyar adawa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
An sha sukar masu ra'ayin sassauci na kasar na Indiya a shafukan sada zumunta tun bayan da jam'iyar Firaminista Narendra Modi ta karbe ragamar mulki a shekarar 2014.
Mutanen da ke saka tufafin kabilu na kamfanin Fabindia da aka saka ko aka zayyana da hannu sun yi ta nuna damuwa - a wani abu da ke nuni da kasa mai rarrabuwar kawuna.
Kamar a wasu wuraren a duniya, kungiyar masu ra'ayin rikau a kasar Indiya na yin fito-na-fito da sassaucin ra'ayi - ta yi amanna cewa masu sassaucin ra'ayin na yin ba'a da kuma kaskantar da su.
Don haka ne Mista Agnihotri ya nuna karara a shafin Tuwita cewa "a ko da yaushe masu goyon bayan Fabindia fuska-biyu gare su…da kan nuna su Indiyawa ne amma ba tare da yin wani abu da ya danganci al'adar Indiya ba''.
Wannan sa-in-sa ce mai cike da damuwa. ''Kwarai, lokacin da Fabindia ya fara sarrafa tufafinsa, na masu kudi ne,'' in ji Radhika Singh, marubuciyar littafin mai lakabin Tufafin Rayuwarmu (Fabric of Our Lives: The Story of Fabindia). An kaddamar da shi ne a matsayin kasuwancin fitar da kayayyaki a shekarar 1960, yana bai wa mazauna karkara kwangilar saka darduman gargajiya.
An rika sayarwa da masu kudin kasar daga babban dakin adana kaya a birnin Delhi a shekarar 1974.
Zuwa karshen shekarar 1990 Fabindia ya bunkasa zuwa sanannen kamfani a tsakanin fadin kasar wanda a kalaman Sunil Sethi, wani dan jarida ya fara nuna yanayin "kamfanin Indiyawa masu karamin karfi."

Asalin hoton, AFP
Tufafi ne da aka saka aka kuma zayyana da hannu, kana aka kawata da wasu alamu na gargajiya. Kamfanin na ikirarin tallafa wa masu sana'oi'n-hannu 55,000 a fadin kasar Indiya.
A idanun jama'a, kamfanin na cikin wani yanayi na sauye-sauye.
A yanzu haka, ya kara bunkasa wajen sayar da kujeru da gadaje, da dardumomi da abincin gargajiya.
Fabindia na bayyana kansa a matsayin "mafi girma a Indiya wajen kayayyakin da aka sarrafa ta hanyar al'adun gargajiya, da kwarewar aikin hannu."
A lokacin da take gudanar da bincikenta a kan kamfanin na FabIndia, Jane Lynch ta gano cewa mutane za su iya "danganta kansu a matsayin masu mu'amala da Fabindia ko kuma tambaya idan na taba kasancewa."

Asalin hoton, Getty Images
Domin tabbatar da cewa ba a taba danganta tufafin Fabindia da "'tufafin zanga-zangar Indiya ba" - muddin duk abin da ke da kyau na sakar-hannu ne da aka bullo da ita lokacin neman 'yancin walwala a matsayin wata alama da ke nuna cewa Indiyawa za su iya dogaro da kan su da auduga, da kasancewa cikin 'yanci daga sayen kayayyaki da tufafin da Turawa ke sayar musu.
Shin ta yaya aka yi Fabindia ya kulla alaka da masu sassaucin ra'ayin kasar Indiya? (Kamfanin ya ki ya amince a yi hira da shi kan wannan labari.)
"Haddasa bacin ran masu ra'ayin rikai ba abu ne mai wahala ko kadan. Idan aka duba labarin Fabindia yana da sarkakiya idan aka yi la'akari da alamu na masu hannu-da-shuni.
Da kuma batun mallaka, ko shakka babu ya taka muhimmiyar rawa. Kamfani ne wanda ba 'yan kasa ne suka kafa shi ba. Don haka shin yana wakiltar wani abu da ya shafe mu?" Shobhaa De, daya daga cikin fitattun marubuta na Indiya ta bayyana cike da mamaki.
Mis De ta yi amanna cewa Fabindia kamfani ne da ke amfana wa wadanda mutanen da ake kira jholawalas, wadanda ke son su fita cikin adon tufafin gargajiya masu kyau da kuma tsada."

Asalin hoton, Getty Images
Sanjay Srivastava, wani farfesan halayyar dan adama a Jami'ar Kwalejin London, y ace ana danganta Fabindia kungiyar masu sana'oin hannu da jam'iyar Congress ke mu'ala da ita a lokacin da ta ke kan mulki, kana tufafin da tufafinsu ne 'yan boko akasari masana kimiyyar halayyar zamantakewar dan adam da ke sukar lamirin Mista Modi ke amfani da shi''.
Har ila au, duka mutanen da ke saka tufafin Fabindia a matsayin masu ra'ayin sassauci na adawa da jam'iyar Mista Modi da akidunta, ka iya kasa gano inda aka nufa.
Da dama sun ce sun yi matukar mamaki kan dalilin da ya sa magoya bayan Mista Modi za su zabi caccakar kamfanin wanda ke samun kayansa daga dubban masu fasahar hannu a yankunan karkara - shi kan sa firaministan ya saka Indiya a cikin muhimman shirinsa na masana'antu.
Kamfanin ya yi shirin bayar da kyautukan hannayen-jari fiye da masu fasahar sana'ar hannun da manoma a lokacin da ya ci kasuwar hannayen-jarinsa ta biyu nan gaba kadan cikin wanna shekarar.
"Babban kamfani ne. Tufafinsa sun kuma zama na bai-daya. Ya kasance wata alama mai sauki ga masu ra'ayin sassauci," in ji Mista Desai.












